Ministan albarkatun gona da raya karkara, Sabo Nanono ya ce ƙasar nan ta na noma abinci mai yawan gaske da zai iya ciyar da al’ummar ƙasar baki dayansu, saɓanin labarin da wasu ke yaɗawa na cewa akwai yunwa a wasu ɓangarorin ƙasar nan.
Nanono ya bayyana hakan ne a gurin shirye-shiryen bikin ranar abinci ta duniya wacce za’a gudanar ranar 16 ga watan Oktoba.
Ministan ya ce, ko shakka babu kuskure ne mutum ya rinka fadin cewa akwai yunwa a ƙasar nan. Sai dai kawai ana iya cewa akwai wata ‘yar tangarda da gwamnatin tarayya ke kokarin magancewa a karkashin hukumar lura da abinci ta duniya.
“Daga abinda nake gani cikin dakin taron nan , babu wata alamar yunwa, sai dai masu kiba kawai nake gani wanda ba mamaki wasu kibar tasu ma tayi yawa. Kudurin gwamnatin tarayya a yanzu shi ne mu rinka noma abinda zamu ci da kanmu”
“Zan iya cewa muna noma abinda zamu ci kuma babu yunwa a ƙasar nan, amma dai idan kuka ce ‘yar tangarda da ba’a rasa ba zan yadda gaskiya. Abinci a ƙasar nan yana da matukar araha sosai fiye da sauran ƙasashen duniya”
“A Kano zaka iya cin abinci da naira 30 kacal kuma ka koshi. A ganina kamata yayi mu godewa Allah da ya bamu ikon noma aboncin da za mu iya ciyar da kanmu kuma babu tsada a kasar nan.” Inji Ministan.
Da yake magana akan rufe kan iyaka kuwa, Ministan ya ce, manoman shinkafa da sauran kayan amfani sunyi murna matuka da rufe kan iyakar. Ya kuma ce duk da cewa mutane da dama ba su ji dadi ba amma abinda ya biyo bayan rufewar labarine mai dadi.