Ƙarin Albashi Ba Zai Taimaki Ma’aikata Ba – Sanata Makarfi

156

Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Ahmed Makarfi, ya ce, neman karin albashi da ma’aikata ke yi ba shi ne abu mafi muhimmanci ba wanda zai taimake su, in da ya buƙaci ma’aikatan gwamnati su mayar da hankali wajen tilasta gwamnati yin aiki bisa gaskiya da adalci.
Kazalika, ya bayyana cewa, akwai buƙatar a samar da abubuwan more rayuwa da za su rage yawan kudin da ma’aikata ke kashe wa a wata.
Makarfi, wanda kuma tsohon sanatan ne daga Jihar Kaduna, ya fadi hakan ne yayin taron tsofin daliban makarantar hadaka ta tarayya (USOSA) da ke garin Kaduna.
Tsohon gwamnan jihar Kadunan ya kuma yi gargadi akan ba wa kudi fifiko cikin tsarin aikin gwamnati a ƙasar nan, ya ce kamata ya yi ma’aikata su bukaci shugabanni su gudanar da jagorancin gwamnati bisa gaskiya da riƙon amana saɓanin neman ko da yaushe a kara musu kudi.
“Kudi ba za su yi wa ma’aikata wani amfani ba. Na san da wannan ƙalubalen tun kafin na zama gwamnan jihar Kaduna, kuma su ma shugabannin kungiyar kwadago sun san da hakan,” in ji Maƙarfi.
“Saɓanin neman karin kuɗi kowanne lokaci, kamata ya yi ma’aikata su bukaci shugabanni su gudanar da jagoranci bisa adalci, su nemi a inganta harkokin tsaro, a samar da abubuwan more rayuwa, su nemi abubuwa daga wurin hukuma da za su saukaka mu su rayuwa da yawan kashe kudi.
“Amma idan kullum kudi ka ke bukata, sai wani ya ba ka Naira 10, amma ya dauke ma ka Naira 30. Da me ka karu kenan?”

Rahoton Leadership Hausa

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan