Ba Zan Iya Auren Yawale A Zahiri Ba; Sabo Da Bana Son Kishiya – Rayya

361

Jarumar wasan kwaikwayon nan Surayya Aminu wadda akafi sa ni da Rayya a shirin film din Kwana Casa’in ta bayyana cewa ita fa a zahiri ba za ta iya auren abokin wasanta Yawale ba, domin kuwa Yawalen yana da mata, ita kuma ba ta son kishiya, sannan kuma ba shi da kudi alhalin ita kuma mai kudi take so.


Cikin wata tattaunawa da Rayyan ta yi da Freedom Radio ta ce “Yawale abokin aikina ne, Yawale yana da mata ni kuma bana son kishiya, amma da ace ma bashi da mata, ni nafi karfin Yawale, don bashi da kudi, ni kuma mai kudi nake nema”.


Sai dai bayan da Freedom Radio ta sanya wannan tattaunawa acikin shirin ta na Indaranka a kwanakin baya, jarumar ta fito ta janye wannan magana da tayi a shafinta na Instagram kamar yadda zaku ji a jawabinta dake kasa.

Rahoton Freedom Radio Kano.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan