Gasar Ahlan Pre Season Ta 2019 Ta Bar Darussa Da Dama

161

An kammala gasar wasannin share fage na Dr. Ahlan karo na uku gasar da akayiwa lakabi da Ahlan Pre Season Tournament.

Saidai gasar ta bar darussa da dama ga kungiyoyin kwallon kafan da suka fafata wannan gasa ta 2019 da darussa ga masu kallo.

Ga jerin wasu daga cikin darussan kamar haka:

  1. Gasar ta bayar da darasi wajen karancin jefa kwallaye agasar domin awasan farko na bikin bude gasar Plateau United ce ta casa Pillars daci 1 da nema, hakama awasan karshe na gasar kwallo 1 aka jefa inda Nasarawa United ta lashe El Kanemi Warriors daci 1 da nema.
  2. Wasu manyan kungiyoyin kwallon kafan kodaga rukuni basu fitoba kamar zakarun gasar Kano Pillars da Katsina United da Lobi Stars da kuma Abia Warriors.
  3. Ansami kungiyar kwallon kafan datake buga gasar ajin kwararru tayi namijin kokari wato Rarara inda harsai datakai matakin wasan kusa dana karshe tare da sabuwar kungiyar data hauro gasar ajin Premier ta kasar nan wato Jigawa Golden Stars.
  4. Wasan share fagen ya kara samun karbuwa a Najeriya da Afrika baki daya duba da irin yadda aka fadada kwamitin gasar.
  5. Manyan masu horas wa daga manyan kungiyoyin kwallon kafa a Najeriya sun halarci jahar Kano alokaci guda kamar su Audu Maikaba da Usman Abdallah da Stanley Egunma da Gbenga Ogunbote da sauransu. Haka manyan masu ruwa da tsaki aharkar kwallon kafa a kasar nan sun taru a jahar Kano waje daya kamar wanda ya assasa gasar Dr. Sharu Rabiu Inuwa Ahlan da shugaban gasar Bar. Isaac Danladi da Ahmad Yusuf Fresh da Auwal Baba Jade da General coordinator na gasar wato Jude da babban maga takarda a hukumar shirya league ta kasa da Shehu Dikko da sauransu.
  6. Wajen alkalancin gasar anyi alkalanci mai nagarta domin kuwa ga babban misali har mai horas war kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars aka kora daga filin wasa kuma akaci tararsa kudi naira 50,000 wanda a Kano akeyi kuma akayiwa mai horas da kungiyar datake daga Kano haka, wannan ya nuna cewar akwai alkalanci mai kyau a gasar.
  7. Ansami walwala ta ‘yan wasan da sukazo daga sassan kasar nan awannan gasa da aka kammala.
  8. Wannan gasa ta nuna cewar bawai kawai kwallon kafa kadai ake bugawa ba domin masu horas wa sun zagaya wasu makarantun a Kano domin koyar dasu haka ankai tallafi gidan marayu da kuma yadda Rabiu Ali Pele Captain na Kano Pillars dayaziyarci makaranta har yake yiwa dalilai nasiha cewar kada su saka kansu aharkar shaye shaye da daba domin ba abune mai kyau ba.
  9. Ansami darasi na awasan kusa dana kusa dana karshe dukkanin wasanni 4 da aka fafata sai a bugun daga kai sai mai tsaron gida akayi nasara wannan ya nuna cewar kungiyoyin kwallon kafan karfinsu yazo daya kenan.
  10. Salon gasar ya sauya gaba daya akan gasoshin baya da akayi domin ansami cigaba sosai.

Daga karshe wasan da aka gudanar na karshe tsakanin kungiyoyin kwallon kafan Nasarawa United da El Kanemi Warriors yayi kyau sosai inda Nasarawa United ta lashe gasar daci 1 da nema akaron farko.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan