Ina Saka Mata A Fim Ɗi Na Ne Domin Kar Su Je Su Yi Karuwanci – Adam Zango

161

Fitaccen jarumin nan na fina-finan Hausa Adam A. Zango ya karyata wani ‘malami’ da ya yi ikirarin cewa jarumin yana neman mata ‘yan kasa da shekara 20 da zummar tantance su domin ya sanya su a wani sabon fim dinsa.
Malamin, wanda aka nuno shi a wani bidiyo yana huduba, ya ce jarumin ya fice daga masana’antar Kannywood ne saboda ba ya so hukumomi su tace fina-finansa da niyyar bin tsarin “tarbiyyar addinin musulunci”.
Ya ce jarumin yana neman mata ‘yan kasa da shekara 20 domin ya sanya su a fim da zummar lalata tarbiyarsu da kuma hana hukumomin tace fina-finai yin aikinsu.
A bidiyon da Adam Zango ya wallafa domin martani ga malamin, jarumin ya dauki Alkur’ani mai tsarki, ya zargi malamin da “yin karya akan abin da bai sani ba.”
“Na rantse da Allah duk abin da malamin nan ya fada a kaina karya ne.
“Duk yarinyar da ka ga na saka a cikin fim dina ita ta kawo kanta ko kuma na ga wasu sun saka ta a fim ni ma na sanya ta.
Idan kuma sabuwa ce ta kawo kanta sai na tabbatar da izinin iyayenta kafin na saka ta.”
Jarumin ya kalubalanci malamin da ya fito da shaidar cewa yana kai ‘yan mata cikin otal-otal.
Ya kara da cewa yana sanya mata a cikin fim dinsa ne domin kada su je su yi karuwanci ko su lalace.
Adam Zango ya yi kira ga manyan malami irin su Sheikh Ahmad Gumi da Sheikh Ibrahim Daurawa da Sheikh Abubakar Giro Argungu, wadanda ya ce ba za su yi wa’azi irin wannan a kan sa ba tare da hujja ba, da su ja masa kunne.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan