Babban Sakataren Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa, NLC, Emmanuel Ugboaja, ya ce har yanzu Ƙungiyar Ƙwadago ba ta fitar da wata sabuwar sanarwar yajin aiki ba bisa zaton gaza cimma yarjejeniya da Gwamnatin Tarayya kan yadda za a gyara mafi ƙarancin albashi.
Da yake ƙarin haske game da tattaunawar sulhu da suke ci gaba da yi da Gwamnatin Tarayya a Abuja a jiya da daddare, ya ce abinda sanarwar farko ta ce shi ne Ƙungiyar Ƙwadago ba za ta iya tabbatar da tafiyar al’amura daidai a ma’aikatu ba, idan, bayan 16 ga Oktoba, 2019, Gwamnatin Tarayya ba ta dawo da taron tattaunawar sulhu ba.
“Ƙungiyar Ƙwadago tana da sauran hanyoyi na nuna fushinta, yajin aiki yana zama matakin ƙarshe ne kawai”, in ji Mista Ugboaja.
A tattaunawar da suka yi ranar Talata, dukkanin ɓangarorin biyu sun amince za su ci gaba da tattaunawa a yau Laraba da ƙarfe 2:00 na rana.