Muna So A Ɗauki Tsattsauran Mataki Ga Waɗanda Suka Sace Yaran Kano- Ibo

209

Kusan kwana biyar da ceto yaran Kano da wani gungun masu garkuwa da mutane su shida suka yi garkuwa da su, al’ummar Ibo a jihar sun yi Allah-wadai da abin da kakkausan harshe.

Idan dai ba a manta ba, Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta yi holin mutum shida da ake zargi da laifin sace wasu yara tara ‘yan jihar Kano, inda suka kai su jihar Anambra, suka canza musu addini zuwa Kiristanci suka kuma canza musu sunaye tare da siyar da su.

A wata sanarwa da suka sanya wa hannu ranar Laraba, Shugaban Ƙungiyar ‘Yan Kasuwa ta Ibo a Kano, Cif Ebenezer Chima da Sarki Al’ummar Ibo na Kano, Igwe Boniface Ibekwe, al’ummar ta Ibo sun yi kira da a yi hukunci mai tsanani ga waɗanda suka yi garkuwa da yaran.

Sanarwar ta yabi jami’an tsaro bisa yadda suka ɗauki mataki a kan lokaci da kuma dabara abinda ya haifar da ceto yaran.

“Muna bada shawara da a yanke wa waɗannan mutane hukunci mai tsanani don ya zama darasi ga saura waɗanda za su so su yi irin wannan mummunan aiki”, in ji sanarwar.

Sanarwar ta kuma yaba wa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II da al’ummar Kano bisa yadda suka nuna fahimta.

Ta kuma yi kira ga al’ummar Ibo dake Kano da su ci gaba da harkokinsu na yau da kullum a jihar.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan