Kungiyar kwallon kafa ta Nasarawa United ta zamo zakara agasar Ahlan Pre Season Tournament da aka kammala a yau Laraba.
Ta zamo zakara ne bayan ta doke kungiyar kwallon kafa ta El Kanemi Warriors daci 1 da nema.

Wannan shine karo na 3 da aka gudanar da wannan gasa ta Ahlan Pre Season Tournament inda a 2017 da 2018 Kano Pillars nw sune suka zamo zakara amma a wannan gasar karo na 3 kungiyar kwallon kafa ta ta Nasarawa United ne suka zamo zakara.
An bayyana wannan gasa ta Dr. Sharu Rabiu Inuwa Ahlan amatsayin wasan share fage da babu kamarsa a fadin nahiyar Afrika.
Har ila yau an bayyana wannan gasa amatsayin karamar Premier ta Najeriya.

Abubakar na na El-Kanemi Warriors ne yafi kowa jefa kwallaye a gasar.
Bala Nkiyu ne na Nasarawa United ya zamo gwarzon mai horas wa.