A Cikin Wata Ɗaya, Mun Ci Tarar Mutum 5000- KAROTA

181

Hukumar Kula da Zirga-Zirgar Ababen Hawa ta Jihar Kano, KAROTA, ta ce ta kama mutum 5000 da laifi a cikin wata ɗaya kacal ta hanyar kotunta ta tafi-da-gidanka.

Shugaban Hukumar, Baffa Babba Dan’Agundi ya bayyana haka a ofishinsa ranar Laraba lokacin da yake karɓar baƙuncin mambobin Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Ƙasa, NUJ, Reshen Jihar Kano.

Mista Dan’Agundi ya kuma bayyana shirin da hukumar ke yi na ɓullo da aikin al’umma ga masu karya dokokin hanya waɗanda ba za su iya biyan tara ba.

“Kun san, ɗaya daga cikin ƙalubalen da muke fuskanta shi ne idan ka kama wasu daga cikin waɗannan masu karya dokokin tuƙin, sai su ce maka ba su da kuɗi. Koda yake KAROTA ba Hukumar Tara Kuɗaɗen Shiga ba ce, abinda ya dame mu shi ne masu amfani da hanya su kiyaye dokokin tuƙi.

“Saboda haka, muna so mu shigo da wannan aikin al’umma ne a matsayin hanyar horo, saboda haka idan ka ce ba ka da kuɗin da za ka biya tararka, za a sa ka ka yi wani aikin al’umma wanda zai yi daidai da girman laifin da ka aikata”, in ji shi.

Ya ƙara da cewa KAROTA tana wayar da kan mutane kan yadda za su ƙaurace wa karya dokokin hanya, waɗanda ya ce hakan ke jawo cunkoson ababen hawa na ba gaira ba dalili da kuma haɗura.

Mista Dan’Agundi ya lissafa wasu daga cikin laifukan da suka haɗa da tsayawa inda bai dace ba, tuƙin ganganci, karɓa ko yin kiran waya a yayin tuƙi, gudu da sauran laifuka masu dangantaka da haka.

“A sakamakon matakan da muke ɗauka tunda na zo a matsayin Manajan Daraktan KAROTA, yawan haɗura da ake samu a cikin birnin Kano ya yi ƙasa da kaso 70 cikin ɗari.

“Wannan ba bayani ne da aka ƙirƙiro ba. Bayanan suna nan har a asibitoci. Lokacin da na ziyarci wasu daga cikin asibitocin jihar nan sun tabbatar min da haka.

“An samu wannan ‘yar nasara ne saboda ƙara wayar da kan ma’aikatanmu waɗanda a shirye suke a yanzu su yi aiki don ci gaban mutane da jiharmu”, in ji shi.

Ya ci gaba da cewa: “In faɗa muku ma, su kan su masu amfani da hanyoyi a yanzu suna kula da dokokin hanya. A watan Yunin wannan shekara, a misali, mukan samu Naira Miliyan N5.5 a matsayin tara daga masu karya dokokin hanya, amma a watan Yuli, mun iya samun Naira Miliyan N2 a matsayin tara daga waɗanda suke karya dokokin hanya”.

Mista Dan’Agundi ya yi kira ga masu amfani da hanya da su riƙa kula da dokokin hanya su kuma bi su, yana mai cewa hakan don kare lafiyar mutane ne.

“Idan dukkaninmu za mu yi abinda yake dai-dai a kan hanya, aikin KAROTA zai zama kaɗan kuma al’umma za su ji daɗin haka”, a kalamansa.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan