Da Yawan ‘Yan Najeriya Ba Su Iya Rera Taken Najeriya Ba- Lai Mohammed

247

A ranar Alhamis ne Ministan Yaɗa Labarai, Lai Mohammed, ya ce da yawan ‘yan Najeriya a yau ba sa iya rera taken Najeriya ko kuma su rera taken alƙawarin ƙasa.

Mista Mohammed, wanda ya bayyana haka a Abuja a wani taron gabatar da jawabai na Mindshift Advocacy for Development Initiative, ya ce da yawan ‘yan Najeriya ba sa yin biyayya ga Kundin Tsarin Mulkin Ƙasar nan, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Ministan ya samu wakilcin wani darakta a Ma’aikatar Yaɗa Labarai, Samuel Soughul.

Ya ce duk da ƙoƙarin Gwamnatin Tarayya na saita ƙasar nan don ci gaba, wasu ‘yan tsiraru a cikin al’umma na ƙoƙarin daƙile wannan ci gaba.

Mista Mohammed ya ce: “Ina jin muna ci gaba. Ba zan ce duka ba, akwai wasu ‘yan tsiraru a cikin al’ummarmu waɗanda ke kawo tazgaro a cikin tsarin ci gaba.

“Bari mu fara daga tushe. Idan kana son ƙasarka, dole ka so duk wani abu da yake da alaƙa da ƙasarka. Ka so ƙasarka, kuma ka so al’ummar ƙasarka. Ka so kayayyakin gwamnati.

“Taken Najeriya, wasu daga cikinmu ba za su iya karantawa ba, ba za su iya rerawa ba, kuma ba za su iya rubutawa ba. Shin kuɗin ƙasar ne, naira da muke wulaƙantawa? Shin Kundin Tsarin Mulkin ne da ba ma bin tanade-tanadensa? Muna da abubuwa da yawa da za mu faɗa, amma har yanzu gaba za ta yi kyau”.

A cewar ministan, ta hanyar bin alƙawarin ƙasa, ‘yan Najeriya ba za su samu matsaloli a kewaye da gidajensu ba, ba za a buƙaci motoci masu sulke ba, kuma ‘yan Najeriya za su kasance masu lura da junansu.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan