Wani rahoto ya ce Hukumar Tattara Kuɗaɗen Shiga ta Ƙasa, FIRS, ta ba Shugaban Majalisar Dattijai, Sanata Ahmad Lawan guraben aiki har na mutum 26 daga mazaɓarsa, jaridar Daily Trust ta gano haka.
Wannan yana zuwa ne a dai-dai lokacin da badaƙalar ɗaukar aiki ke ƙaruwa a Majalisar Dattijan inda wasu sanatoci ke barazanar garƙame majalisar saboda tsarin raba guraben ayyuka da hukumar ta Gwamnatin Tarayya ta bayar.
An ce tuni Shugaban Majalisar Dattijan ya raba wa mutanesa takardun ɗaukar aiki.
Wani sanata da ya zanta da Daily Trust ya zargi Sanata Lawan da “karkatar da gurabe 26 ba tare da lura da sauran sanatoci ba, hatta daga jiharsa ma”.
A jiya wata ƙungiyar matasa mai suna Unity for Collective Progress Forum ta ce dukkan waɗanda suka amfana da ɗaukar aikin sun karɓi takardunsu na kama aiki, kuma ana sa ran “za su fara aiki nan bada daɗewa ba”.
Ƙungiyar ta bada bayanan ƙananan hukumomin da waɗanda suka amfanan suka fito daga mazaɓar Sanata Lawan kamar haka, Nguru, mutum 5; Karasuwa, 3; Machina, 4; Bade, 7; Yusufari, 4; da Jakusko 3.
A jiya, ƙungiyar nan mai fafutikar ganin an yi dai-dai a shugabancin al’umma, wato Socio-Economic Right and Accountability, SERAP, ta buƙaci Sanata Lawan da ya yi ƙarin haske kan zargin da ake yi cewa an ba Shugabannin Majalisar guraben aiki na mutum 100 daga hukumomin Gwamnatin Tarayya.
Mai magana da yawun Shugaban Majalisar Dattijan, Ola Awoniyi bai amsa kiraye-kirayen waya da aka yi masa ba, bai kuma bada amsa ga rubutaccen saƙo da aka aika masa jiya da daddare ba.
Haka shi ma, mai magana da yawun Hukumar Samar Da Guraben Ayyuka ta Ƙasa, FCC, bai amsa kiran waya ba da aka yi masa ba game da batun.
Da yake zantawa da Daily Trust, Shugaban Kwamitin Majalisar Dattijai na Kula da Daidaito Wajen Ɗaukar Aiki da Huɗɗa da Gwamnatoci, Danjuma La’ah, ya ce kwamitin ya fara bincike bisa wannan tsarin nuna bambanci a ɗaukar aiki da wasu hukumomin Gwamnatin Tarayya ke yi.
“Ina yin bincikena a ƙarƙashin ƙasa don kar in kunyata mutane”, in ji shi.