Sata Da Bautar Da Ƙananan Yara: Ina Mafita? Kawu Sule Rano

224

A satin daya gabata ne al’umma Jihar Kano suka tsinci kansu cikin rudani da tashin hankali bayan da Rundunar ‘Yansanda reshen Jihar ta samu nasarar cafke wasu gungun barayin yara ‘yan asalin kabilar Ibo.

Rahotanni sun tabbatar da cewar wasu daga cikin yarannan sun share akalla shekara biyar a Jihar Anambra dake kudu maso gabashin wannan kasa baya da aka saida su ga wasu mutanen na daban. Haka nan an canza musu sunaye daga sunaye su na asali zuwa na wata kabila sannan aka tilasta masu shiga addinin kirista duk da cewar kafatanin wadannan yara musulmi ne masu kananan shekaru.

Babban abin takaicin shine yadda wadannan yara suka manta yaren su wadda hakan ya tilastawa iyayen su kokawar yin amfani da gurbataccen turanci (broken) don magana da ‘ya’ yan su na cikin su.

ABIN DUBAWA
Abin dubawa dai a yanzu shine batun nan na kwato hakkokin iyaye dana wadannan yara. Ko ba’a fada ba kowa yasan iyayen wadannan yara sun yi fama da kuncin rashin sanin halin da yaran su ke ciki. Lalai an sha jigilar nema, anyi kuka, an kwana ba tare da rintsawa ba, anyi zulumi kuma anyi fama da hawan jini.

Su kuwa yaran Allah ne kadai yasan irin ukubarda suka sha domin binciken masana ya tabbatar irin wadannan yara da aka sata azaba na fuskantar cin zarafi kama daga azabtarwa, bautarwa zuwa fyade da sauran su.

Jama’ar Kano kuwa sai nace mun dade muna ganin irin wadannan masifu na batan dabon kananan yara domin kuwa Allah ne kadai yasan adadin yara da irin wadannan mutane suka sace.

ABIN MAMAKI
Abinda ke ba kowa mamaki a yanzu shine yadda Kafafen watsa labarai musamman na kudu da aka sani da kwarmato akan laifukan makamantan wadannan sukayi gum da bakin su tamkar labarin bai isa gare su ba.

Haka na shugabannin mu na arewa, rukunin lauyoyi da sauran masu rajin kare hakkin bil’adama suma dai basu ba wannan batu muhimmancin daya dace da shi ba.

INA MAFITA?
Izuwa yanzu dai mafita ta farko itace mutane su sanya idanu sosai akan kai-komon ‘ya’yan su. Lokaci yayi da zaki daina barin yaranku na gararanba a kwararo ba tare da rakiyar wani babba ba.

Haka nan dole mu sanya idanu akan baki dake kai-komo a unguwannin mu tare da kai rahoto ga hukumomin tsaro game da mutane da muke da shakku akan su.

Yanzu dai hankali ya koma kan hukumomi domin ganin hobbasar da zasuyi wajen kubutar da sauran yaran dake hannun ire-rien wadannan azzaluman mutane tare aiwatar da hukunci akan wadanda aka kama. Mu kuma zamu cigaba da bibiya.

Kawu Sule Rano
Malami Ne A Sashen Nazarin Halayyar Ɗan Adam Na Jami’ar Bayero Da Ke Kano.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan