Zan Zo In Nuna Muku Inda Za Ku Iya Siyan Abincin N30 A Kano- Nanono

185

Alhaji Sabo Nanono, Ministan Aikin Gona ya nace kan cewa mutane a jihar Kano za su iya siyan abincin N30, yana mai alƙawarin zuwa da kansa don ya nuna musu inda za su iya siyan abincin mai arha.

Mista Nanono ya jawo ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta bayan da ya yi iƙirarin cewa babu yunwa a Najeriya.

Labarai24 ta ruwaito cewa Mista Nanono ya bayyana haka ne a wani taron manema labarai a Abuja ranar Litinin don Bikin Ranar Abinci ta Duniya wadda ake bikinta ranar 16 ga Oktoba.

“Ina jin a halin yanzu muna samar da isasshen abinci da muke ciyar da kanmu, kuma ina jin babu yunwa, amma idan ka ce matsaloli, zan yadda.

“Idan mutane suka yi magana game da yunwa na kan yi dariya saboda ba su san yunwa ba. Idan ku ka je sauran ƙasashe, za ku ga abinda ake nufi da yunwa”, in ji Mista Nanono.

“A zahiri yunwa na nufin mutum ya yi kwana goma bai ci komai ba.

Ministan ya ƙara da cewa abinci yana da arha a Najeriya idan aka kwatanta da sauran ƙasashe.

“A Kano misali, za ka iya cin abincin N30 kuma ka ƙoshi. Saboda haka, ya kamata mu gode wa Allah da muke iya ciyar da kanmu, kuma muna da abinci mai arha a ƙasar nan”, in ji shi.

Biyo bayan ce-ce-ku-cen da maganganun nasa suka jawo, ministan ya ce kuskure ne ‘yan Najeriya su riƙa yayata cewa akwai yunwa a ƙasar nan, yana mai jaddada cewa yunwa ta gaske tana nufin mutum ya yi kwanaki goma ba tare da ya samu abinda zai ci ba.

“Zan iya zuwa Kano in nuna muku inda za ku siyi abincin N30 kuma ku ƙoshi. Mutane ba su san ma’anar yunwa ba. Amma suna nema wa kansu annoba ta hanyar yin iƙirarin cewa muna fama da yunwa.

“Yunwa ta gaske tana nufin mutum ya yi kwana goma ba tare da ya samu abinda zai ci ba”, ya faɗi haka a wata sabuwar tattaunawa da Freedom Radio.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan