Jami’an Hukumar Hukunta Masu Yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati, EFCC sun cafke tsohon gwamnan Jjhar Zamfara, Mahmud Aliyu Shinkafi.
Jami’an na EFCC sun yi dirar mikiya ne a gidan Mista Shinkafi dake Titin Nagogo a Kaduna da misalin ƙarfe 1:00 na ranar Juma’a, sannan suka wuce da shi.
Wata majiya a gidan tsohon gwamnan wadda ba ta so a ambaci sunanta ba ta tabbatar wa jaridar DAILY NIGERIAN kama gwamnan.
Majiyar ta ce iyalin gwamnan ba su san inda aka kai Mista Shinkafi ba.
Lokacin da aka tuntuɓe shi, mai magana da yawun EFCC ya ce yana buƙatar lokaci ya yi bincike kafin ya bada amsa game da wannan batu.
“Bari in bincika in ba ka amsa”, in ji shi.
A ranar Alhamis, EFCC ta gabatar da shaidu uku a ci gaba da ƙarar tsohon Ministan Kuɗin, Bashir Yuguda, tsohon gwamnan jihar Zamfara, Mahmud Aliyu Shinkafi, Aminu Ahmed Nahuche da Ibrahim Mallaha a gaban Mai Shari’a Fatima Aminu ta Babbar Kotun Tarayya, Gusau.
EFCC ta gurfanar da waɗannan mutane huɗu ne gaban kotu bisa zargin su da karɓar zunzurutun kuɗi har Naira Miliyan N450 daga hannun tsohuwar Ministar Albarkatun Man Fetur, Diezani Alison-Madueke domin canza alƙiblar zaɓukan 2015.