Masu Yawan Shan Shayi Sun Fi Lafiyar Ƙwaƙwalwa – Binciken Masana

6282

Farfesa Feng Lei ƙwararren malamin lafiyar ƙwaƙwalwa a tsangayar ilimin magani na Yong Loo da ke jami’ar Singapore ya bayyana cewa shan shayi na da muhimmanci ga lafiyar ƙwaƙwalwa.


Haka zalika Farfesa Feng Lei ya ƙara da cewa shan shayi akai-akai na hana mutuwar ƙwaƙwalwa sakamakon tsufa.


“Sakamakon binciken da muka samu hujja ta farko da ke nuna gudunmuwar da shan shayi ke baiwa ƙwaƙwalwa. Kuma hakan na nuna cewa shan shayi sosai na rage rikicewar da yawan shekaru ke kawowa.”


Bincike a baya ya nuna cewa shan shayi na da muhimmanci ga lafiyar dan Adam, kuma amfanin ya kunshi kare cutar zuciya.


A ƙarshe binciken ya nuna cewa shan shayi kullum na rage rikicewar da tsufa ke janyowa da kashi 50%.

Turawa Abokai

3 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan