Manoma Sun Fi Kowa Yawan Jima’i – Binciken Masana

223
spinasieland spinasie landery arbeiders, kleinboere

Wani bincike da aka wallafa a jaridar ”Daily Mirror” ta Birtaniya ya bayyana cewa yanayin aikin da mutum yake yi na tasiri matuka ga rayuwar jima’insa.


Binciken wanda wani kamfani a Birtaniya mai suna ”Lelo” ya gudanar ya tambayi kusan mutum 2,000 maza da mata kan yanayin rayuwar jima’insu da kuma irin ayyukan da suke yi na neman halaliya.


Sakamakon binciken ya nuna cewa manoma ne suka fi yawan jima’i da kusan sama da kashi 33 cikin 100 inda suka ce suna jima’i a kalla sau daya a rana.


Wadanda suka zo na biyu a binciken su ne masu zanen taswirar gine-gine wato ”architects” inda kusan kashi 21 cikin 100 suka shaida cewa su ma a kalla sau daya a rana suke jima’i.

A wani bangaren kuma, binciken ya nuna cewa ‘yan jarida su ne wadanda ba su cika yin jima’i ba inda kashi daya cikin biyar suka ce suna yi a kalla sau daya a wata.


Haka zalika su ma lauyoyi ba a bar su a baya ba domin kuwa binciken ya nuna cewa su ne wadanda ake shan wahala kafin gamsar da su yayin jima’i inda kusan kashi 27 cikin 100 suke karyar gamsuwa yayin jima’i ko da kuwa basu gamsu ba.


Kate Moyle, wacce kwararra ce a kamfanin Lelo a Birtaniya ta bayyana cewa ”Duk da a cikin rukunin masu aiki iri daya akwai kamanceceniya na wasu dabi’u tsakanin mutane, yakamata mu gane cewa akwai kuma banbance-banbance kwarai dagaske musamman a rayuwar jima’insu.


”Sai dai abin da yakamata mu gani shi ne abin da ke gudana, misali kamar yadda manomi ke motsa jiki a gona ya bambanta da na ma’aikaci da ke zaune a ofis wanda hakan zai iya kawo bambanci a karfinsu da kuzarinsu.


”Yanayin aikinmu kamar sa’o’in da muke dauka muna aiki da kuma yanayin wurin aikin kansa na tasiri matuka a rayuwarmu baki daya, ba lallai sai rayuwar jima’inmu ba.”

Rahoton BBC Hausa

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan