Muna Son Yin Sulhu Da Gwamnatin Najeriya- Shi’a

253

A ranar Asabar ne a Katsina Ƙungiyar Gwagwarmayar Musulunci ta Najeriya, IMN, wadda aka fi sani da Shi’a ta miƙa goron gayyata ga gwamnatin Najeriya zuwa teburin sulhu don warware batutuwa da rashin fahimta da suka sa gwamnatin ta haramta aikace-aikacenta.

Shugaban Shi’a ta Katsina, Malam Yahaya Yakubu, wanda ya bada wannan sanarwa yayinda yake yi wa manema labarai jawabi a wani ɓangare na bukukuwan Tattakin Kwana Arba’in wanda suke yi don tunawa da rasuwar Husaini, jikan Annabi Muhammad, ya ce koda yake ƙungiyar ta ɗaukaka ƙara bisa haramta ayyukan nata, kuma tana da tabbacin za ta kayar da gwamnati a karo na 7, suna son a fara tattaunawar sulhu da gwamnati don samun zaman lafiya.

Ya ce: “Koyaushe ƙofofinmu a buɗe suke don tattaunawa da Gwamnatin Tarayya, tayi ne mara sharaɗi don ba gwamnati damar fahimtar mu koda yake dai tuni mun fahimce su, ba mu da wata ƙasa idan ba Najeriya ba”.

A ta bakinsa, “Ba mu da wata hanya da za mu nuna mu bauta wa Allah da ta wuce tattaki na lumana a tituna, kuma ba mu taɓa tayar da hankali ba. Ya kamata Gwamnatin Tarayya ta bada hujja da za ta nuna cewa abinda muke yi kuskure ne ko a wajen Allah. Idan za su iya yin haka za mu daina.

Ya ƙara da cewa: “Muna da kyakkyawar alaƙa da maƙotanmu, kuma muna ma taimakon su idan suna cikin masifa. Mun gayyaci kafafen watsa labarai ne don mu nuna abubuwan da muke yi a fili don haɓaka zaman lafiyar addini da rungumar addinan juna.

Shugaban na Shi’a ya nuna baƙin ciki bisa yadda magoya bayansu ke rayukansu a duk lokacin da suka fito yin tattaki na lumana sakamakon harbe-harben ‘yan sanda, yana mai ƙarawa da cewa ko a kwanan nan, sun rasa a ƙalla mambobi 27 a jihohin ƙasar nan daban-daban.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan