Aboki Mai Wahalar Samu A Wannan Zamanin – Sheikh Aminu Daurawa

56

Abokai iri uku ne :
1- Abokin tayi daɗi, abinda ya kawo shi abota da kai domin ya amfana da kai, ranar da yaga babu amfanin zai kama gabansa.
2- Abokin aiki, wannan abota da shi, iya wajan aiki ne da zarar an kammala aiki shi ke nan sai kowa ya kama gaban sa.
3- Abokin mai daraja mutunci, wanda zai kasance tare da kai, a dukkan mawuyacin hali, ko ka na da shi ko babu, shi yana Ƙaunarka saboda Allah kawai, ba domin wani abu na duniya ba.

Wannan irin abokin yana da wahalar samu, idan ka samu irin sa ka riƙe shi da kyau.

Idan za ka yi abota kayi da masu hankali Domin;
Idan baka nan zasu kare mutunci ka.
Idan basu ganka ba zasu nemeka.
Idan ka samu za su tayaka murna.
Idan kayi kuskure za su gyara maka.
Idan za su yi addu’a ba zasu manta da kai ba.
Idan baka da lafiya za su duba ka su yi maka addu’a.
Idan ka shiga wani hali za su nuna damuwa da alhini.
Idan sun ganka suna murna.
Idan kayi kuskure za su yi maka gyara, cikin hikima.
Idan za’a cuce ka za su taimake ka.
Idan ka mutu zasu yi maka addua, kuma su taimaki iyalanka a bayanka.
Wanda ya rasa abokai na gari yayi asara.
Allah ka bamu abokai na gari.

Shin muna da irin waɗannan abokan?

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan