Abubuwan More Rayuwa 17 Da Ƙasar Libya Ta Rasa Bayan Shekaru 8 Da Kashe Gaddafi

273

A ranar 20 ga Oktoban shekarar 2011 gwamnatin wucin gadin kasar Libya ta bayyana mutuwan hambararren Shugaban kasar Muammar Gaddafi, sakamakon raunikar da ya samu, lokacin da ake neman cafke shi.


Gaddafi ya gamu da ajalinsa kusa da mahaifarsa garin Sirte, inda dakarun gwamnatin wucin gadi suka kwace iko da garin.


Tun bayan da aka hambarar da mulkin Mu’ammar Gaddafi tare da yi masa kisan gilla kuma kisan wulakanci, ƙasar Libya ta ke fama da tashin hankali tare da kashe-kashen jama’a babu dare babu rana.


Jim kaɗan da yi masa kisan gilla manyan shugabannin ƙasashen duniya sun yi jinjina ga mutuwar Muammar Gaddafi, tare da danganta karshensa a matsayin karshen mulkin kama-karya tare da fatan ganin an gina sabuwar kasar Libya.


Amma abin ya zo da bazata domin la’akari da yadda abubuwa su ka lalace tare da tabarbarewar al’amuran cigaban ƙasar, sakamakon tarzomar da ta ƙi-ci- ta-ƙi-cinyewa.


Abubuwan More Rayuwa 17 Da Al’ummar Ƙasar Libya Su Ka Rasa Bayan Sun Kashe Gaddafi

Mutanen kasar Libya lokacin mulkin tsohon shugaban kasarsu da ‘yan tawaye su ka kashe watau Muammar Ghaddafi na daya daga cikin masu jin daɗi a duk faɗin nahiyar Afrika.


Ga wasu bayanan abubuwan more rayuwa da mutanen ƙasar Libya ke dasu a lokacin mulkin Muammar Ghaddafi kamar yanda yake a ireport na kafar watsa labarai ta CNN.


1- ‘Yan kasar ta Libya basa biyan kudin wutar lantarki: kyauta suke shan wuta.


2- Babu kudin ruwa a bashin da bankunan kasar suke baiwa ‘yan kasa, saboda bankunan kasar duk mallakin gwamnatine.


3- Idan dan kasar Libya ya kammala karatun jami’a, bai samu aiki ba,to gwamnati zata rika biyanshi rabin albashin da ake biyan me takardar karatu irin nashi dake aiki, har sai ya samu aikin yi.


4- Idan dan kasar Libya yana son kama sana’ar noma to gwamnati zata bashi filin noma, da gida, kayan aiki, iri da kuma dabbobin da zai fara dasu duk kyauta.


5- Tsohon shugaban kasar Libya, Muammar Ghaddafi ya gina madatsar ruwa ta noman rani mafi girma a Duniya, a kokarin gano man fetur, kasar ta gano wani ruwa tinjim a wani yanki na kasar, wannan yasa shugaban kasar yayi amfani da wannan damar wajan gina madatsar ruwa wadda babu irinta ko ina a Duniya, an ajiye bututu masu kai ruwan manyan biranen kasar ta Libya.


6- Ƴancin kane dole a baka gidan kanka a ƙasar Libya.


7- Idan mutane sukayi aure a ƙasar ta Libya, gwamnati na basu kudi, dalar Amurka dubu Hamsin, kwatankwacin naira miliyan goma sha takwas dan su fara rayuwa cikin sauki.


8- Ana baiwa yan ‘yan kasar ta Libya wani kaso daga cikin kudin da aka sayar da danyen man fetur din kasa.


9- Idan mace ta haihu, ana bata kyautar kudi, dalar amurka dubu biyar, kwatankwacin naira miliyan daya da dubu dari takwas.


10- Idan dan kasar Libya zai sayi mota, gwamnati ke biya mai rabin kudin motar.


11- Kowace litar man fetur ana sayar da ita akan kwatankwacin naira hamsin a lokacin shugaba Ghaddafi.


12- Da kudi, kwatankwacin naira hamsin da hudu, dan kasar Libya zai sayi biredi guda arba’in.


13- Ilimi da kiwon lafiya kyautane, ga kowane dan kasar Libya, kasar Libya nada mafi kyawu da ingantaccen harkar lafiya fiye da kowace kasar larabawa da ta Africa.


14- Idan dan kasar Libya na bukatar fita kasar waje dan neman lafiya ko kuma ilimi, to gwamnatice zata dauki nauyinshi kuma duk wata za’a rika bashi dalar Amurka dubu biyu da dari uku, kwatan kwacin naira dubu dari takwas.


15- Kasar Libya bata da bashin kowace kasar Duniya a kanta, haka kuma tana da rarar kudi da suka kai dalar Amurka biliyan dari da hamsin, duk da yake cewa yanzu an sakawa kudin takunkumi.


16- Mutane da yawa sun fahimci cewa gamayyar kungiyar tsaro ta turawan yamma sun jagoranci kifar da gwamnatin Muammar Ghaddafine saboda (su saci) man fetur da kuma wasu sauran albarkatun kasa da Allah ya azurta kasar dashi.


17- Ghaddafi ya kasance lokacin rayuwarshi yana ta kira ga kasashen Afrika akan azo ayi takardar kudi ta bai daya wadda zata ragewa dalar Amurka tasiri a yankin nahiyar Africa, amma tun bayan mutuwarshi ba’a kara jin wannan batu ya tasoba.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan