Gwamnan Zamfara Ya Naɗa Mai Tallen Biredi Mataimakinsa Na Musamman

215

Gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawalle, ya amince da nadin wani mai tallen biredi a matsayin mataimakinsa na musamman akan harkokin sabbin kafafen sadarwar zamani.

Matashin mai suna Abdulmalik Saidu Gusau, ya zama matashi na farko wanda ya kere sa’a daga tallar biredi zuwa mai taimakawa gwamna.

Kafin nadin, Abdulmalik ya kasance mai sana’ar sayarda biredi a tashar Bagu dake garin Gusau.

A wani bincike da majiyar mu ta yi, ta gano cewa gwamna Matawalle na jihar Zamfara shine gwamna daya tilo a Arewacin Nijeriya da ya fi sanya matasa cikin gwamnatinsa.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan