Har yanzu Ana cigaba da taraliya da rikakken zakin nan da ya kubuce a gidan Zoo, Rundunar yansanda tace ta zube jami’an tsaro domin samar da tsaro a kowanne bangare na gidan yayin da ma’aikatan dabbobi ke cigaba da ƙoƙarin cigaba da yiwa zakin bindigar bacci.
Da fari dai wasu jaridu sun yaɗa labarin kama zakin amma daga bisani aka bayyana cewar bai kamu ba an dai yi masa allurar bacci ne, Kuma yanzu ya shanye allurar.
Wata majiya ta shaida cewar dukkan alluran sagau, da aka yiwa Zakin ya shanye su, sai an nemi Mai karfi an Kara masa wacce kuma sai an kawo ta daga Abuja
Naso Jin tabbacin Hakan daga bakin kakakin gidan Zoo Amma Bai Sami daga waya ta ba.
Nasiru Salisu Zango
Turawa Abokai