A Ƙarshe Riƙaƙƙen Zakin Nan Da Ya Tsinke Ya Koma Cikin Kejinsa Da Kan Sa

238

Zakin nan daya arce daga cikin Kejin da yake tsare a gidan ajiyar Namun Daji na Kano, Zoo ya koma cikin Gidansa Da safiyar Yau Litinin, Misalin karfe Bakwai saura minti biyu.

Shugaban Gidan Ajiyar Namun Daji na Kano, Sa’id Gwadabe Gwarzo ne ya tabbatar da haka ga wakilinmu Kolawole Omoniyi ta wayar Salula.

Sarkin Dawan ya koma cikin kejinsa ne da Kansa batare da kwararrun da aka gaiyyato daga Abuja sun dauki wani mataki a kansa ba.

Tun ranar Asabar din dai data gabata ce, Zakin ya Kubuce daga cikin Kejinsa , har kuma ta kaiga ya cinye Awaki guda hudu tare da Jimina guda biyu.

Kafin haka dai tuni Mai girma Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya bada umarnin A harbe Zakin Dan shekaru Goma sha biyar, wanda kudinsa ya kai naira Milyan Hudu Lakadan, Matukar ya zama Barazana ga Rayuwar Jama’a.

To sai dai Kuma a halin Yanzu a iya cewa Zakin ya rufa ma kansa Asiri bayan da ya koma cikin Kejin da ake tsare dashi.

Wannan dai shine Karo na biyu a tarihin Kafuwar gidan Ajiyar Namun Dajin da aka samu Zaki yana Kwacewa, To shin ko wane Mataki aka dauka domin maganin haka a nan Gaba?

Rahoton Arewa Radio Kano

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan