Buhari Zai Karɓo Bashin Dala Biliyan Uku Daga Bankin Duniya Don Samar Da Wuta- Ministar Kuɗi

206

A ranar Lahadi ne Ministar Kuɗi, Zainab Ahmed, ta ce Bankin Duniya yana gab da ba Najeriya rancen kuɗi don samun kuɗaɗen da za a tafiyar da ɓangaren wutar lantarkin Najeriya.

Misis Ahmed ta bayyana haka ne a Washington, babban birnin Amurka yayin wani taron manema labarai bisa abubuwan da tawagar Najeriya suka tattauna a Taron Shekara- Shekara na Bankin Duniya da Asusun Bada Lamuni na Duniya, IMF.

“Mun bada buƙatar samar da kuɗi don aikin wutar lantarki a ma’aunin Dala Biliyan $1.5 zuwa Dala Biliyan Huɗu.

“A ƙarshe dai, kamar za mu buƙaci girman bashin da ya kai Dalar Amurka Biliyan Uku wanda za a samar a matakai huɗu, Dala Miliyan $750 kowane mataki.

“Shirinmu shi ne tawagarmu za ta iya zuwa Bankin Duniya domin samun amincewar bada kason farko a cikin Afrilu, 2019”, in ji ta.

Ministar ta bayyana cewa za a yi amfani da bashin wajen cike giɓin kuɗaɗe da bambance-bambancen kuɗin wuta, abubuwan da ta ce masu zuba jari a ɓangaren suke ƙorafi a kai koyaushe.

Idan gwamnati ta iya faɗaɗa bashin zuwa Dala Biliyan Huɗu, za a yi amfani da ƙarin Dala Biliyan Ɗaya wajen rarraba wutar lantarki, a cewar ta.

“Zai taimake mu wajen fita daga tallafi da ake bayarwa a halin yanzu a ɓangaren wutar lantarkin.

“Ya kamata rancen ya gyara ɓangaren wutar lantarki kuma ya dawo da kasuwancin rarraba wutar don ɗora shi a kan kadarko mai ƙwari.

“Za a yi wannan ne don a tabbatar da cewa an ba su isasshen ‘yanci don su fita su samu kuɗaɗen zuba jari don faɗada netwok ɗin rarraba wutar”, a kalaman ministar.

Misis Ahmed ta bayyana cewa samar da waɗannan kuɗaɗe zai haɗa da giɓin dake tsakanin kuɗin wuta da ake biya yanzu da kuma ainihin kuɗaɗen samar da wutar lantarki.

“Zai bunƙasa damarmu wajen biyan basussuka da ake bin mu a ɓangaren waɗanda sun taru, don masu zuba jari a ɓangaren su ci gaba da faɗaɗa zuba jari a ɓangaren.

“Tsarin rarraba wutar lantarkin zai zama a baya idan aka aiwatar da sauran gyare-gyare.

“Zai zama bashi ga kamfanonin rarraba wutar lantarki saboda kamfani mai zaman kansa ne zai mallake su”, in ji ta.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan