Gasar Kofin Sanata Ibrahim Shekarau Daza a Fara

167

An fitar da ranar da za a fara gasar cin kofin Sanata Malam Ibrahim Shekaru mai wakiltar kananan hukumomin dake birnin Kano.

Tunda farko dai an bayyana ranar 6 zuwa 10 ga watan Nuwamba za a fara gasar, amma da aka sake zama na musamman kwamitin gasar suka sake saka sabuwar ranar daza’afara gasar inda aka bayyana cewar sai ranar 20 zuwa 24 ga watan Nuwamba za a fara gasar.

Wakikan Osio da Tee International na Russia da kuma mataimakin shugaban kungiyar kwallon kafa ta Locomotiv Moscow da aka gayyata zasu iso Najeriya a ranar 17 da 18 a watan na Nuwamba inda zasuyi ganawa da Sanata Malam Ibrahim Shekaru a Abuja sannan su tawo Kano aranar 19 ga watan ma Satumba.

Kamar yadda kafofin yada labarai na NTA da AIT da TVC da sauran kafafen yada labarai suka nemi abasu dama domin haska wannan gasa suma kamfanin Wasa.ng da Labarai24 sun nemi abasu damar sushiga ciki domin kawo duk abin da akayi awannan gasa inda zasu buga labaran a kamfanin nasu.

Gasar dai tsohon gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekaru ne ya dauki nauyinta.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan