Ya Kamata Sanata Kwankwaso Ya Daina Tara Mutane Idan Yana Buƙatar Zaman Lafiya – Abba Gwale

219

Magana ta gaskiya yakamata KWANKWASO ya dakatar da tara mutanensa da yake yi idan yana Neman cigaban zaman lafiya a wannan jiha tamu. Idan har zai tara magoya bayansa Idan zaiyi taro tabbas kuwa za’a samu tashin hankali domin wasu abokan adawarsa na siyasa zasu kawowa magoya bayan nasa hari.

Bai kamata a dinga tara magoya baya ba domin yin wani taro haka kawai sannan wasu daga baya su tare musu hanya azo ana saransu da makami ana Neman rayuwarsu.

Lokacin siyasa ya wuce yanzu har an fara mulki, yakamata Kwankwaso yasan cewa ran mutum daya yafi taron da zai hada muhimmanci.

Kwankwaso zai iya bude makarantar daya bude yau ba tare da an tara mutane ba kuma zai iya bikin birthday dinsa shima ba dole sai an gayyaci mutane ba.

Amma mutane su dauki kafa tun daga cikin gari har garin Madobi saboda soyayya sannan kuma azo ana Neman kashesu a banza.

Sai ayi tunani agani tsakanin taron da rayuwar mutum daya wannene yafi muhimmanci, sai a dauki guda daya.

Idan bazaku daina taro ba su kuma masu kawo muku harin bazasu daina kawo waba, tunda hakane Ku sai Ku hakura Ku daina idan har ana son magoya bayan kamar yadda suma suke nuna soyayyarsu.

Tunda yanzu babu mulki a hannunka sai ka hakura, mulki fa ba wasa bane, Idan akaga dama za’a iya hana taron gaba daya kuma babu abinda zai faru saboda gwamnati fa ba wasa bace.

Babu yadda za’ayi kana tara irin wadannan magoya bayan kuma kayi tunanin baka da ‘yan adawa. Kuma wadannan magoya bayan duk saboda kwankwaso suke wannan tafiya, saboda haka hanya daya kaima da zaka biyasu shine kare rayuwarsu da rayukansu ta hanyar daina duk wani taro da zai tara magoya bayan da zasu wuce mutum 500.

Ku kuma magoya baya yakamata kuyi tunani, acikin wadanda aka fitarwa da jini babu Dan kwankwaso ko kuma wani Dan uwansa na jini, duk magoya bayane kawai masu nuna soyayya.

Kwankwaso acikin magoya bayan ka akwai wadanda suke cewa su MAKAFI ne basa ganin kowa sai KWANKWASO, don Allah kai kuma kace su bude idon domin su dinga ganin hanya.

Suma wadanda suka kai harin yakamata su San cewa kowa yanada damar yin taro a kowanne lokaci idan har bai sabawa doka ba Saboda haka bai kamata saboda siyasa a dinga Neman rayuwar mutane ba. Kuma abinda akayi bai kamata ba, anyi zalinci.

Abba Gwale Ɗan Jarida Ne Mai Zaman Kan Sa, Ya Rubuto Daga Birnin Kano.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan