Tun bayan da ministan harkokin gona Sabo Na Nono ya bayyana cewa da Naira 30 za’a iya cin abincin 30 a koshi a jihar Kano.
Batun da ya jawo cece kuce akan wannan batu na cewa sam hakan ba zai taba yiwuwa ba.
A yanzu haka dai an bude wajen siyar da abincin Naira 30 a unguwar Sani Mai nagge layin Kuka dake karamar hukumar Gwale a jihar Kano.
To sai dai lamarin ya sha bam-bam domin kuwa an sami wani magidanci mai suna Haruna Injiniya, wanda ya bude wurin cin abinci akan kudi Naira 30.
Ya ce waccan magana ta ministan gona ita ce ta sanya shi bude gidan abincin, domin al’umma su ci su koshi ba tare da wata damuwa ba.
Ya kuma ce samfarin abincin nasa ya yi shi ne hadin wasa-wasa yadda mutum zai ci ya koshi harma a hada masa da ruwan sha duka a Naira 30.
Sannan ya kuma ce ya na fatan wasu ma za su yi koyi da shi don talaka ya amfana ba tare da ya sha wahala ba.
Rahoton Dala FM Kano