Sanata kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso ya ce gwamnatin Jihar karkashin gwamna abdullahi Umar Ganduje ce ta sa aka kai wa tawagarsa hari a yammacin ranar Litinin, a lokaicn da suke kan hanyarsu ta koma wa birnin Kano daga garin Madobi.
Sanata Kwankwaso ya shaida wa BBC cewa bai yi mamakin faruwar al’amarin bakasancewar sai da suka sanar da rudunar ‘yan sandan jihar rahotan da suka tattara na cewar gwamnati na shirin kai musu hari wajen taron nasu, amma duk da wannan sanarwa babu wani mataki da aka dauka don hana hakan faruwa.
To sai dai BBC ta yi kokarin tuntubar bangaren gwamnatin jihar Kano amma kokarin bai samu nasara ba, inda wakilinmu na Kano, Khalipha Dokaji ya aike da sako ga wayar sakataren yada labaran gwamnan jihar, Malam Aba Anwar, amma ba a samu wani martani ba.
To sai rundunar ‘yan sandan jihar, ta ce ba ta da masaniyar rikicin da bangaren Kwankwasiyya suka yi zargin ya faru.
Mai magana da yawun rundunar, DSP Haruna Abdullahi ya ce “An kira mu mu je Madobi kuma mun tura jami’anmu amma ba su ga komai na faruwa ba.”
Ya kara da cewa “babu wani korafi da muka samu a rubuce ballantana mu bincika saboda haka idan mutum yana da korafi to ya rubuta mana sai mu bincika.”
A ranar Litinin ne dai Kwankwaso da tawagarsa suka je garin Madobi wadda mahaifar sanatan ce domin bude wata kwalejin koyon aikin ungozoma mai zaman kanta.
An ce bayan kammala bude makarantar ne tawagar ta Sanata Kwankwaso ta koma birnin Kano daga inda ayarin ya tashi, kuma da shigar tawagar birnin ne wasu “zauna gari banza dauke da makamai” suka “far wa” tawagar da sara da suka.
Bayanai sun nuna cewa ba a samu rasa rai ba amma an samu jikkata da dama.
Wannan shi ne karo na uku da ake samun arangamar da ta fito fili tsakanin magoya bayan sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da na Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.
Ko a dab da zaben 2019, sai da bangarorin biyu suka gabza a garin Kofa da ke karamar hukumar Bebeji, al’amarin da ya yi sanadiyyar jikkata da kone dukiyoyi.
Har wa yau, magoya ‘yan siyasar biyu sun yi arangama da juna a fadar mai martaba Sarkin Kano, Sarki Muhammad Sanusi lokacin hawan Daushe a bara.
Hamayya tsakanin Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da Gwamna Abdullahi Ganduje dai kullum kara ruruwa take yi tun bayan da bangarorin biyu suka raba gari.
Rahoton BBC Hausa