Yau Arsen Wenger Yake Bikin Cika Shekaru 70

48

Ayau Talata 22 ga watan Oktoba tsohon mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal kuma dan asalin kasar France wato Arsen Wenger yake bikin cika shekaru 70.

Wenger dai ya kafa tarihi da dama kafin ya jingine harkar horas wa.

Ga irin bajintar da Arsen Wenger yayi kafin yabar harkar horas wa:

  1. Arsen Wenger ya kwashe shekaru 22 yana jagorantar kungiyoyin kwallon kafa amatsayinsa na mai horas wa.
  2. Arsen Wenger ya jagoranci kungiyoyin kwallon kafar daya horas har wasanni 1,235.
  3. Daga cikin wasannin daya jagoranta ya lashe wasanni 707.
  4. Sannan kungiyoyin daya jagoranta sunjefa Kwallaye 2,298.

Amatakin nasarar lashe kofuna kuwa:

Wenger ya lashe gasar kalu-bale wato FA da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal guda 7.

Sannan Arsen Wenger ya lashe gasar ajin Premier ta kasar Ingila tare da Arsenal har sau 3 inda daga cikin ukun harda wanda aka baiwa Arsenal a filin wasa na Manchester United wato Old Trafford da kuma filin wasa na kungiyar kwallon kafa ta Tottenham Hotspur wato White Hart Lane.

Haka zalika Wenger yakai kungiyar kwallon kafa ta Arsenal matakin wasan karshe a gasar zakarun nahiyar turai a 2006 inda sukayi rashin nasara a hannun Barcelona daci 2 da 1.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan