Home / Wasanni / Da Yiwuwar Mourinho Yakarbi Ragamar Horas Da Dortmund

Da Yiwuwar Mourinho Yakarbi Ragamar Horas Da Dortmund

Akwai yiwuwar tsohon mai horas da kungiyoyin kwallon kafan Porto da Chelsea da Inter Milan harma da Real Madrid wato Jose Mourinho yakabi ragamar horas da kungiyar kwallon kafa ta Brussia Dortmund dake kasar Jamus.

Hakan ya biyo bayan rashin kokari da mai horas da kungiyar yake nayanzu wato Favre.

Ayanzu dai Brussia Dortmund na matsayi na 4 a gasar Bundes liga ta kasar Jamus inda kuma suka buga gasar zakarun nahiyar turai guda biyu suka buga kunnen doki awasan farko da Barcelona inda wasa na 2 suka sami nasara.

Ayau dai da daddare Brussia Dortmund zata kara wasa da kungiyar kwallon kafa ta Inter Milan agasar zakarun nahiyar turai.

Shin idan Mourinho ya karbi ragamar horas da Brussia Dortmund ko wasan hamayyar nan da akeyi tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich da Dortmund mai taken Daclassica zai kara tsami?

About Suraj Naiya Kudiddifawa

Check Also

Aubameyang ya kamu da cutar Maleria

Sai dai Har ya zuwa yanzu Arteta bai iya ba da sanarwar ranar dawowar ɗan wasan gaban ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *