Kimanin ‘Yan Najeriya Miliyan 50 Na Da Taɓin Hankali- Ƙwararre

173

Dakta Ibrahim Wakawa, Shugaban Asibitin Kula da Masu Taɓin Hankali na Gwamnatin Tarayya dake Maiduguri, CMD, ya ce a ƙalla ‘yan Najeriya miliyan 50 ne ke fama da cutar taɓin hankali.

Mista Wakawa ya bayyana haka ne ranar Laraba a Maiduguri yayin ƙaddamar da wani Shirin Gwamnatin Jihar Borno na Taimaka wa Masu Cutar Taɓin Hankali mai taken Borno State Government Mental Health Strategic Implementation Plan a Turance.

Wanda ya samu wakilcin Dakta Ibrahim Mshelia, wani Ƙwararren Likita a asibitin, Mista Wakawa ya danganta cutar taɓin hankali da ta yi yawa a ƙasar nan da rikice-rikicen ‘yan tada ƙayar baya, rashin wayar da kai da kuma rashin kayan aikin laifiya da za a tunkari irin waɗannan matsaloli.

CMD ɗin ya ce bincike-bincike sun nuna cewa a cikin ‘yan Najeriya huɗu, ɗaya yana fama da cutar taɓin hankali da dangoginta.

Ya bayyana cewa asibitin yana kula da kimanin mutane miliyan 30 a Arewa Maso Gabas da sauran yankunan ƙasar nan.

“A ƙalla kaso 60 cikin ɗari na mutanen dake zuwa cibiyoyin kula da lafiya matakin farko suna da cutar taɓin hankali.

“Za a iya bada cikakkiyar lura da kulawa ga cutar taɓin hankali a cibiyar kula da lafiya matakin farko”, in ji Mista Wakawa.

Ya yaba wa gwamnatin jihar Borno bisa ƙoƙarinta na kafa tsare-tsare dake da nufin sauƙaƙa harkar lafiya ga kowa.

Dakta Owili Collins, Manajan Bada Kulawar Gaggawa na Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO a Najeriya, ya ce hukumar tana aiki da gwamnatocin jihohi da ta tarayya don inganta lafiyar ƙwaƙwalwa ta hanyar bada tallafi daban-daban.

Wnada ya samu wakilcin Issac Bwatin, Jami’in Kula da Masu Taɓin Hankali na WHO, Mista Collins ya ce hukumar ta ba ma’aikatan cibiyoyin kula da lafiya matakin farko kimanin 154 hor game da alamomin da za su gane cutar taɓin hankali da bayar da ayyukan jin ƙai ga mutanen da rikicin Boko Haram ya shafa.

Ya ce WHO ta karɓi tallafi daga Tarayyar Turai don ɗaga darajar tare da yi wa Asibitin Kula da Masu Taɓin Hankali na Gwamnatin Tarayya dake Maiduguri kwaskwarima don inganta aikace-aikacensa ga jama’a.

“WHO tana aiki a kan shiri mai dogon zango da jihar Borno da Gwamnatin Tarayya don sauya yadda ake lura da cutar taɓin hankali a ƙasar nan ta hanyar aiwatar da shirin da kuma tallafi a cikin tsarin.

Ya ce abubuwa kamar rashin tabbas, damuwar da take biyo bayan rasa matsugunai da rasa aikin sun sa mutane da yawa sun kamu cutar da taɓin hankali.

“Rikicin ‘yan tada ƙayar baya a Arewa Maso Gabas ya sa mutane da yawa sun samu cutar taɓin hankali”, in ji jami’in na WHO.

Ya lissafa damuwa da ruɗewa a matsayin wasu abubuwa dake kawo cutar taɓin hankali.

Deborah Magdalena, Shuagabar IOM Mental Health and Psychosocial Support, wata ƙungiya mai tallafa wa masu taɓin hankali, ta ce ƙungiyar ta fara taimaka Najeriya tun shekarar 2015.

“IOM a shirye take ta ci gaba da samar da tallafi kamar yadda tsari ya tanada don rage tsana da kuma nuna bambanci da ake nuna wa mutanen da suka samu taɓin hankali, ta kuma bunƙasa girmama ɗan Adam” in ji ta.

Salisu Kwaya-Bura, Kwamishinan Lafiya da Ayyukan Jin Ƙai na Jihar Borno, ya ce an tsara wannan abin kirki ne don samar da cibiyoyin kula da masu taɓin hankali don samar da ingantacciyar lafiya ga dukkan al’ummar jihar.

Wanda ya samu wakilcin Babban Sakatarensa, Ibrahim Kidah, Mista Kwaya-Bura ya ce gwamnatin jihar ta faɗaɗa ƙoƙari wajen kula da cutar taɓin hankali tun 2017.

“Shirin aiwatarwa yana samar da dabaru masu faɗi inda ake mayar da hankali ga haɗa kula da cutar taɓin hankali a dukkan matakai, kula da taɓin hankali, bada magani da gyaran hali”, in ji shi.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan