Kotu Ta Hana IGP Ci Gaba Da Ɗaukar Sabbin ‘Yan Sanda Aiki

176

A ranar Laraba ne Babbar Kotun Tarayya dake Abuja ta umarci Babban Sifeton ‘Yan Sanda na Ƙasa, IGP Mohammed Adamu da Hukumar Kula da ‘Yan Sanda, PSC, da su tsaya yadda ake game da ci gaba da ɗaukar ‘yan sanda 100,000 aiki.

Mai Shari’a Inyang Ekwo ya bada wannan umarni a yayin sauraron ƙarar da Hukumar ‘Yan Sanda ta shigar da Babban Sifeton na ‘Yan Sanda.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN, ya ruwaito cewa PSC ta kawo ƙara kotun ne, inda take roƙon ta ta hana IGP ci gaba da ɗaukar sabbin jami’an ‘yan sanda kimanin 100,000 da ya fara, tunda tana ganin ya shigar mata hurumi.

Daga nan sai alƙalin ya ɗaga ƙarar zuwa 4 ga Nuwamba don duba cancanctar ƙarar.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan