Rufe Iyakokin Ƙasar Nan Da Aka Yi Akwai Kuskure – Bello Sharaɗa

269

Kashi tamanin na duk abin da muke amfani da shi na rayuwa a kasar nan, sai mun tsallaka kasashen ketare muke sayo shi. Da abinci da sutura da magani da kowane irin karfe da sauran kayan amfanin yau da kullum ko dan China ne ko India ko dan Cotonou. Fetur ma da muke hakowa anan sai mun kai shi Turai sannan a sarrafa shi a dawo mana da shi.

Najeriya babbar kasuwa ce a duniya. Akwai sama da mutum miliyan 200, sabulun wanka kadai da ake amfani da shi ya ishi wata kasar arziki. Gamu da yawa, ga fadin kasa ga dimbin albarkatu duk da haka a wata kididdiga Najeriya ce birnin talauci na duniya.

Abincin da muka fi ci ita ce shinkafa. Muna sayo ta daga kasar Indiya da Thailand da Amurka. Muna noma ta Hausa, amma yawanmu yafi karfin mu iya ci da kanmu, saboda har yanzu dabarun noman mutanen da muke amfani da su. Duk shekara muna cin tan miliyan takwas da rabi na shinkafa. Iyakar kuma abin da muke iya nomawa tan miliyan biyar zuwa shida. Ko wasu manyan kasashe kamar China suna sayen shinkafa domin cike gibin abin da suke nomawa. A bara da ta gabata wato 2018, shinkafar da China ta saya daga waje ta kai ta naira biliyan 700.

A zangon farko na PMB 2015 ya maida hankali da tsaurara matakan shigo da shinkafa da kuma baiwa CBN dama ta habaka noman shinkafa. Shugaban kasa yana ganin ya samu nasara don haka a wannan zangon yake ta sake-saken, kwata kwata a daina shigo da shinkafa ta iyakokin Najeriya na kasa, banda na ruwa, banda kuma na sama.

Ana shigo da kaya zuwa Najeriya ta halastatun iyakokin da muke da su na kasa a Seme da Badagry a Lagos da Ilela a Sokoto da Kamba a Kebbi da Kongom da Daura da Jibiya a Katsina da Maigatari a Jigawa da Mubi a Adamawa da Tabkin Chadi a Borno da kuma wasu da yawan gaske. Muna da iyaka da kasar Benin da kasar Kamaru da kasar Ghana da kasar Nijar da kuma manyan tekun Ginuea da Lake Chad.

Kayan da ake shigowa da su Najeriya akasari ana auno su tun daga Turai da Gabas ta tsakiya da Asiya da Amurka da Latin Amurka zuwa tashar ruwa ta Lome a kasar Togo ko Port Novo ta Cotonou a kasar Benin. Akwai tashoshin ruwa a Lagos da Calabar da Port Harcourt, amma ‘yan kasuwa sun fi gamsuwa da na Togo da Benin. Sun gwammace su kai kayansu wadancan tashoshin sannan daga bisani a dauko su a manyan motoci a biyo da su ta kasa zuwa Najeriya.

Damuwar da Najeriya take da ita shi ne, jami’an kwastam su na zargin ta wadannan hanyoyin kasa ne ake shigo da makamai da miyagun kwayoyi cikin Najeriya. Sannan kuma Najeriya bata samun cikakken amfani na haraji, makota sun fi cin gajiyar cinikin kasa da kasa. Na karshe kuma yawancin kayan da ake shigowa da su Najeriya, musamman shinkafa, muna nomanta amma kuma babu isasshiyar riba ga manoma. A ganinsu kuma kudaden Najeriya na zurarewa a wajen canjin dala.

Misalin da aka fi yawan fada shi ne, kasar Benin gaba dayanta ba ta kai Kano ba a yawan jama’a, akwai mutum miliyan 11, amma kuma sune na farko a Afirka da suka fi sayen shinkafa. To me suke yi da wannan dimbin shinkafar? A 2018 da kadan kasar Benin tafi China a wajen cin shinkafa. China ta sayo ta dala biliyan daya da miliyan 200, ita kuma Benin ta sayo ta dala miliyan 950, ta ninka abin da Amerika ta saya sau uku, sannan ta ninka wanda Najeriya ta saya sau biyar. Ma’ana dai shinkafar da ake kawo ta kasar Benin, yan Najeriya ne suke cinye wa don mabukatanta sun fi yawa.

Da goyon bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari da sahalewar CGC Hameed Ali ranar 21 ga Augusta 2019 aka rufe wasu iyakokin Najeriya. An ware mako uku ne za a yi wani aiki na musamman. Daga nan kuma sai aka kara tsawon lokacin, sannan ya hada da wasu sabbin iyakokin. Daga karshe kuma aka ce an rufe bodar gaba daya ba rana balle wata na budewa.. Hukumar kwastam tace ta gano rufe bodar akwai riba mai gwabi, don har an tara naira biliyan 115 cikin kwana 40. Kuma jama’ar kasashe makota suna dandana kudarsu a sakamakon matakin da suka dauka. Yanzu sun ce duk mai son shigo da wani kaya ko dai ya bi ta sama ko ta ruwa ko kuma duk kayan da za a wuce da shi ta kasa da yan rakiyar kasashen ECOWAS to Najeriya sai ta yi masa binciken kwakwaf. SHARUDAN BUDE BODA KENAN.

Shin garkame bodar dabara ce kuma hanya mai bullewa? Dama kuma haka ya kamata?

A fahimtata, rufe bodar nan akwai gyara. In kun rufeta, kayan masarufi zasu yi tsada, shinkafar da ake magana akanta ta gidan ta fara faskara. NBS hukumar kididdiga ta kasa, ta fitar da lissafin hawan farashi na watan Satumba, har tana cewa a wata biyar baya kullum farashi kasa yake yi, amma daga rufe bodar ya hau sosai.

Abu na biyu da aka rufe bodar kuma sai aka hana sauran kayan bukatu sukuni, wanda ba haramci akansu, suma mutane matafiya aka garkame su. A tsarin duniya na yau, ba zai yiwu a rufe boda kawai don iko, akwai ka’idojin ciniki da yarjejeniyoyi na WTO, ECOWAS, AfCTA da UNCTAD bai yiwuwa rana tsaka ka take su ka wuce, in ka yi haka zasu shafeka da jama’ar kasarka.

Da yawa mutane suna cewa haka China ta yi. Sam, irin salon da Mao Tse Tung ya yi, wanda muke kokarin sai lallai mun bi shi, da aka shiga ukubarsa sai da mutane miliyan 18 suka mutu, ba girma ba arziki aka bude kofa aka watsar da shi, shi ne fa China ta samu kanta. Da UAE wato Dubai da kasar Singapore sune mafi kyawun misalin harkar bude boda da su za a yi koyi da su. Don nasu ya bada natija.

Abu na uku, rufe boda ba zai dawwama ba, tunda ba zai dore ba, in aka bar shi zai iya illa babba. A maimakon haka a kirkiro hanyoyin zamani da za a dakile fasa-kwauri. Ko shugaban kasar Amurka Trump da yake kokarin rufe bodar America da Mexico ai ya san zance ne kawai. Ba zata rufu ba, an yi barazana kuma an ja kunne.

Abu na hudu farfado da tattalin arzikin Najeriya da bunkasa shi ba harkar dare daya bace, kuma ba harkar soja ko kwaminisanci ba ce. Dabara ce da lissafi na shekaru, yana bukatar nutsuwa ba harmagaza ko zafin kai ba. Dole a gina abin da zai yi wu ko bayan ba Buhari da APC ko wa zai hau kan mulkin Najeriya a gobe.

Abu na karshe duk kyawun tsari da alfanunsa in dai ba zai kawo wa mutane sauki da walwala ba da kwanciyar hankali sunansa aikin kawai.

Muhammad Bello Sharaɗa Ya Rubuto Daga Kano

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan