‘Yan Najeriya Sun Jikkata A Sabbin Hare-Haren Ƙin Jinin Baƙi A Afirka Ta Kudu

31

‘Yan Najeriya uku na daga cikin ‘yan ƙasashen waje da sababbin hare-haren ƙin jinin baƙi da aka kai a wurare daban-daban a Witbank, a Lardin Mpumanlaga na Afirka ta Kudu suka rutsa da su ranar Talata, a cewar wata ƙungiyar ‘yan Najeriya.

Kakakin Ƙungiyar ‘Yan Najeriya Mazauna Afirka ta Kudu, NUSA, Odafe Ikele, ya faɗa wa Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN ta wayar tarho daga Witbank cewa a ranar Talata da sassafe ne aka fara kai hare-haren.

Haren-haren na ranar Talata na zuwa ne duk da ƙoƙarin da Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya da Cyril Ramaphosa na Afirk ta Kudu ke yi na ganin sun kawo ƙarshen waɗannan hare-hare da ake kai wa baƙi a ƙasar, musamman ‘yan Najeriya.

Wannan ƙoƙarin ganin an samu zaman lafiya ne ya sa aka ga Shugaba Buhari ya ziyarci Shugaba Ramaphosa, har kuma suka yi taro da al’ummar Najeriya mazauna ƙasar ta Afirka ta Kudu.

“Wasu gungun mutane ne da suka haɗa da direbobin tasi suka je yankuna daban-daban a Witbank, suna kai hare-hare ga kamfanonin ‘yan ƙasashen waje da kuma baƙi.

“‘Yan Najeriya uku sun jikkata, amma ba labarin rasa rai kawo yanzu. Wasu daga cikin ‘yan uwanmu ‘yan Najeriya na neman mafaka Ofishin ‘Yan Sanda na Witbank”, in ji Mista Ikele.

A cewar NUSA, har yanzu ‘yan Najeriya uku da hare-haren suka rutsa da su suna neman mafaka a Ofishin ‘Yan Sanda na Witbank.

Har yanzu ba a samu bayanai filla-filla na yadda al’amarin ya kasance ba, amma NUSA ta kuma ce ‘yan sanda a yankin sun kawo ɗauki, kuma sun gargaɗi mutane da su ƙaurace wa Babban Lardin Kasuwanci a garin.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan