A Cikin Wata Takwas, Mun Mayar Da Biliyan 11.68 Ga Lalitar Gwamnati- NIS

163

Hukumar Kula da Shige da Fice ta Najeriya, NIS, ta ce a cikin wata takwas, ta mayar da fiye da Naira Biliyan 11.68 da kuma Dalar Amurka $22,972 zuwa lalitar gwamnati.

Kwanturola Janar, CG na NIS, Muhammad Babandede ya bayyana haka a Taron Ƙara wa Juna Sani na Shekara-Shekara na Kwanturola Janar ranar Alhamis a Benin.

Mista Babandede ya ce NIS ba kawai wata babbar hukumar tsaro ba ce ta gwamnati, amma hukuma ce mai hidimta wa ƙasa kuma mai samar da kuɗaɗen shiga.

“A 2018, mun mayar da jimillar N6,945,585,360 da kuma $36,909,411 ga Gwamnatin Tarayya a matsayin kasonta na kuɗaɗen shiga da ta tara ta hanyar ayyukan Haɗin Gwiwa Tsakanin Gwamnati da Masu Zaman Kansu, PPP.

“Wannan shekara, daga 1 ga Janairu zuwa 31 ga Agusta, mun mayar da N11,682,009,761 da $22,972.38 zuwa lalitar gwamnati.

“Kowane jami’in shige da fice, mai ci ko wanda ya yi ritaya, ya yadda sosai cewa sake duba hanyar PPPs zai ninka ko ruɓanya kuɗaɗen shiga sau uku a lokacin da muke amfani da kasafin kuɗi mai giɓi.

“Kar a canza min maganata.

“Na yi amanna da PPP saboda yana kiyaye kuɗaɗe kuma yana inganta nagartar aiki, amma ba wasu PPPs da muke aiki da su ba waɗanda ke tatse dukiyarmu kuma ba sa ƙara wa aikinmu wani abin kirki”, in ji shi.

CG ɗin ya ce yana sane yana kuma da ƙwarin gwiwar cewa Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola zai kawo canji ta hanyar sabunta wasu PPPs ɗin.

Ya ce taron shekara-shekarar ya zama wani taron tattara dabaru wanda yake ba hukumar damar duba aikace-aikacenta ta kuma nemo sabuwar hanya, ta kuma fito da dabaru, manufofi da shirye-shirye.

“Taron na Shekara-shekara ya ci gaba da tallafa wa hukumar wajen cimma manya-manyan nasarori, inganta ayyukanmu, ya kuma bunƙasa imanin da jama’a da ƙasashen duniya su ka yi da hukumar a matsayin iyalin NIS”, in ji Mista Babandede.

Kamar yadda majiyar Labarai24 ta tabbatar, taken Taron Bana na Kwanturola Janar da Hukumar Kula da Shige da Ficen shi ne: “Tafiyar da Hukumar Shige da Fice a Tattalin Arziƙi Mai Tasowa: Rawar da NIS ka iya takawa”.

Taron na Shekara-shekara ya samu halartar Gwamman Edo, Godwin Obaseki; Ministan Harkokin Cikin Gida, Kwanturola Janar masu ritaya, Mataimaka Kwanturola Janar da sauransu.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan