Ya Kamata A Sauƙaƙawa Matasa Lefe – Malama Ladi

465

Wata tsohuwar kwamandar Hisba bangaren mata a karamar hukumar Dala Malama Ladi Sulaiman Gwammaja ta roki iyaye mata su saukakawa matasa a bangaren lefe.

Ladi Sulaiman ta yi wannan rokon ne a wani taron karfafawa kungiyoyin addinin musulinci da suke fita yada addinin musulunci a kananan hukumomi 44 da hukumar Shari’ar musulunci ta jihar Kano ta shirya.

Ta ce matasan da su ka yi aure suna fuskantar tarin matsaloli bayan da aka mika amarya dakin ta, musamman bangaren cimaka da kulawar yau da kullum.

Tace za ka ga matasa sun cika akwatinan lefe har 7 an kawo, sai kuma kaga watakila mijin bai kammala gina muhalli da za’a tare ba.

Kwamandar ta kara da cewar, ko a bikin wani matashi da suka yi a kwanakin baya, abokan sa sun hada dubu 200 domin biyan kudin wajen liyafa, amma ango bashi da rigar kirki da zai sanya yaje daurin auren sa.

Wannan ta sanya masu hangen nesa a cikin abokan suka yanke shawarar siya masa kayan abinci, tare da guzurin wasu kudaden domin cefanen yau da gobe.

Wannan itace rayuwa da matasa suka tsinci kai a yau, don haka ta yi kira ga samari da iyaye da ‘yan mata da su rinka saukakawa juna don samun zaman aure mai daurewa.

Rahoton Dala FM

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan