‘Yan Najeriya 75,000 Ke Garƙame A Gidajen Yari- Aregbesola

166

A ranar Laraba ne Ministan Harkokin Cikin Gida na Najeriya, Rauf Aregbesola, ya ce akwai ‘yan Najeriya mazauna gidan yari har 75,000 dake garƙame a gidajen yarin ƙasar nan.

Mista Aregbesola ya bayyana haka ne a wani taron al’umma da Kwamitin Kasafin Kuɗi na Majalisar Dokoki ta Ƙasa ya shirya.

Ministan ya ce Gwamnatin Tarayya tana ƙoƙari wajen rage cunkoso a gidajen gyaran hali a faɗin ƙasar nan ta hanyar rage yawan mazauna gidajen da ke jiran shari’a.

Ya ce sabuwar dokar da Shugaba Muhammadu Buhari ya sanya wa hannu ba kawai ta canza sunayen gidajen yari zuwa cibiyoyin gyaran hali ba ne, amma ta ba jami’ai dama kada su karɓi masu laifi da ke jiran shari’a idan girman gidan ba zai iya ɗaukar su ba.

“Abinda muke yi game da mutanen da ke jiran shari’a, dokar ta yi tanadin a ƙi karɓar duk wani mutum da aka kawo daga kotu, wanda ke jiran shari’a.

“To, da wannan sabuwar doka, a fili yake cewa nan gaba ba za mu samu abinda muke da shi ba yanzu a gidajenmu na gyaran hali”.

Ya ce bisa buƙatar da ake da ita na rage cunkoso a gidajen yari, gwamnati ta kafa Kwamitin Rage Cunkoso A Gidajen Yari.

Mista Aregbesola ya ce kwamitin yana nan yana ta aiki da Ministan Shari’a na Ƙasa don rage cunkoso a gidajen gyaran hali na ƙasar nan.

“Nan ba da daɗewa ba, za mu rage batun jiran shari’a sosai; saboda muna nan muna aiki da gwamnoni a kan haka.

“Saboda kusan kaso 90 cikin ɗari na mazauna gidajen yari da ke jiran shari’a waɗanda su ka keta dokokin jihohi ne, saboda haka wannan nauyin gwamnatocin jihohi ne daban-daban.

“To, da akwai buƙatar mu yi tafiya tare da su wajen samo hanyoyin da za a rage cunkoso a gidajen gyaran halin, kuma ina so in tabbatar mana cewa nan da wata shida, za mu manta da wannan”.

Ministan ya ce gwamnati da gaske ta ke ta rage wa gidajenta na gyaran hali matsin lamba, ta kyauta kula da mazauna gidajen yarin, musamman wajen gyara halayensu, dawo da su kan turba da kuma kuma saita su yadda za su yi rayuwa ta daidai idan sun kammala zamansu na gidan yari.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan