A ranar Laraba ne Ministan Matasa da Bunƙasa Wasanni na Ƙasa, Sunday Dare, ya ce za a ƙara alawus ɗin Matasa Masu Yi wa Ƙasa Hidima zuwa N30,000.
Mista Dare ya bayyana haka ne a shafinsa na Twitter.
Ya ce Darakta Janar na Hukumar Kula da Matasa Masu Yi wa Ƙasa Hidima, NYSC, Birgediya Janar Shu’aibu Ibrahim zai yi bayanin yadda sabon alawus ɗin zai kasance bayan Ma’aikatar Kuɗi da Ma’aikatar Matasa da Bunƙasa Wasanni sun yi masa bayani.
Ya rubuta a shafinsa na Twitter: “Mako mai kamawa, DJ na NYSC zai yi bayanin sabon ‘alawee’ na Matasa Masu Yi wa Ƙasa Hidima bayan ya samu cikakken bayani daga Ma’aikatar Kuɗi da Ma’aikatar Matasa da Bunƙasa Wasanni”.
A ranar 18 ga Afrilu, 2018 ne gwamnatin Najeriya ta amince za ta fara biyan N30,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi, kuma ranar Juma’a da ta gabata, ta cimma yarjejeniyar da Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa, NLC bisa yadda ƙarin albashin zai kasance, bayan an shafe watanni ana tattaunawa.
A ranar Laraba, taron tattaunawa na Majalisar Zartarwa ta Ƙasa, wanda Mataimakin Shugaban Ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya jagoranta ya bada wa’adin da za a fara biyan sabon mafi ƙarancin albashin.