An Cafke Mutum Uku A Zamfara Sakamakon Ta’ammali Da Giya

191

Hukumar Shari’a ta Jihar Zamfara ta cafke mutum uku bisa laifin siyarwa da shan barasa a yankin Tudun Wada da ke Gusau, babban birnin jihar.

Babban Sakataren Hukumar, Dakta Atiku Zawiyya ya bayyana haka yayinda yake holin masu laifin a gaban manema labarai a hedikwatar hukumar da ke Gusau ranar Alhamis.

Mista Zawiyya ya ce an cafke mutanen uku ne bisa wani rahoton sirri da wasu ‘yan ƙasa na gari daga yankin su ka kai wa hukumar.

Ya ce an cafke Lydia Samuel, John Samuel da mahaifiyarsu, Madam Maria a gidansu da kwalaben giya 103 da kuma jarkoki biyu ɗauke da burkutu.

Mista Zawiyya ya ce ana kan bincike a halin yanzu, kuma da an kammala za a gurfanar da mutanen a kotu.

Ya yi kira ga al’ummar jihar da su taimaka wa hukumar da sauran hukumomin tsaro da kyawawan bayanai da za su taimaka wajen gano laifuka a jihar.

Mista Zawiyya ya ce dokar da ta kafa hukumar, waɗanda aka yi wa kwaskwarima, ta ba ta iko ta kama, ta yi bincike sannan ta gurfanar da duk wani mutum da ake zargi da aikata laifi a kotu.

Ya yi kira ga gwamnatin jihar da ta samar wa da hukumar taimako ta ɓangaren ma’aikata da dabaru don ba ta damar aiwatar da aikace-aikacenta yadda ya dace.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan