INEC Ta Kashe Miliyoyin Kuɗi Ba Tare Da An Amince Mata Ba

141

Kwamitin Haɗa Gwiwa na Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, na Majalisar Dokoki ta Ƙasa, ya nuna damuwa bisa ƙarin kuɗi da INEC ta kashe ba tare da neman izini daga Majalisar Dokoki ta Ƙasa ba.

An gano haka ne a yayin da hukumar ta kare kare kasafin kuɗinta na 2019/2020.

Ibrahim Babangida daga Katsina ne ya tayar da maganar lokacin da ya tambayi Shugaban INEC, Farfesa Mahmud Yakubu ya yi bayanin me ya sa hukumar ta yi gaban kanta wajen kashe ƙarin kuɗaɗe da ba sa cikin kasafin kuɗin da majalisar ta sahale mata.

Ya ce abinda hukumar ta yi ya saɓa da Kundin Tsarin Mulkin 1999 wanda ya yi tanadin cewa ba za a kashe kuɗaɗe ba idan dai ba sa cikin kasafin kuɗi ba tare da izinin Majalisar Dokoki ta Ƙasa ba.

Fred Agbedi, ɗan majalisa mai wakiltar Bayelsa, shi ma ya tambayi Shugaban na INEC da ya faɗa wa kwamitin dokokin da hukumar ta dogara da su wajen kashe kuɗaɗe da ba sa cikin kasafin kuɗi.

Ya ce duk da buƙatar gaggawa da ta ke iya tilasta hukumar ta kashe kuɗaɗe da ba sa cikin kasafin kuɗi, irin waɗannan kashe-kashen kuɗi ya kamata a yi su ne ta hanyar neman izini daga Majalisar Dokoki ta Ƙasa.

Wasu daga cikin yankunan da kwamitin ya gano hukumar ta kashe ƙarin kuɗaɗe su ne: aikace-aikacen tsaro, inda aka amince ta kashe Naira Miliyan N150, amma hukumar ta kashe Naira Miliyan N194.8.

Haka kuma, Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta amince hukumar ta kashe Naira Miliyan 100 wajen hayar ofis, amma hukumar ta kashe Naira Miliyan N232.1 kamar yadda ta kashe Naira Miliyan N440.8 ga aikace-aikace na gaba ɗaya, inda Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta amince mata ta kashe Naira Miliyan N342,000,000, da dai sauran kashe-kashen kuɗaɗe da ba sa cikin kasafin kuɗi.

Da yake jawabin kariya, Shugaban na INEC ya ce an kashe waɗannan kuɗaɗe ne sakamakon buƙatun gaggawa da su ka taso, kuma hakan yi daidai da ‘yancin hukumar na aiwatar da aikace-aikacenta.

Da yake jawabi game da ma’aikatan hukumar, Mista Mahmud ya ce har yanzu hukumar ba ta ɗora ma’aikatanta a Tsarin Biyan Albashi na Bai Ɗaya Ba, wato IPPIS.

Ya ce har yanzu hukumar tana jiran takardar da za ta yi mata bayanin yadda za ta aiwatar da tsarin na IPPIS.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan