Kwastam Ta Ƙwace Shinkafa Da Kuɗinta Ya Kai Miliyan 3.5 A Kaduna

220

A ranar Juma’a ne Shiyyar ‘B’ ta Hukumar Hana Fasa Ƙwauri ta Ƙasa ta ce ta ƙwace buhuhunan shinkafa ‘yar waje guda 149 da aka shigo da ita ba bisa ƙa’ida ba da kuɗinta ya kai Naira Miliyan N3.5.

Mai magana da yawun hukumar, Abubakar Usman ya bayyana haka a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Kaduna.

Mista Usman ya ce an ƙwace shinkafar a tashar mota ta Mando yayinda ake juye ta a buhuhunan gida, inda za a kai ta Legas.

Ya ce jami’an hukumar sun kai samame ne zuwa wajen, bayan samun rahoton sirri, amma ya ce ba a cafke kowa ba.

“Hukumar za ta ci gaba da yin iya ƙoƙarinta wajen gudanar da aikace-aikacenta. Hukumar Kwastam za ta iya wannan aiki, kuma ‘yan simoga ko masu ba su goyon baya ba za su tsorata ta ba.

“Za mu ci gaba da yin ƙwace mu kuma tabbatar da cewa ‘yan simoga sun ci gaba da yin asara har sai sun daina haramtaccen kasuwanci”, in ji Mista Usaman.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan