Sun Ƙwace Mana Kasuwanci, Sun Yi Mana Fashin Mutuncin ‘Ya’yanmu

173

Gaskiyar Marigayi Sa’adu Zungur da ya ce, “Bahaushe Ba Shi Da Hankali Zai Sha Wahala Nan Duniya”

Baya ga mamaye Kasuwar Sabon Gari daya daga cikin unguwa mafi tsada a jihar Kano. Kaso 7 cikin 10 na kasuwancin wajen Inyamurai ne. Kama daga harkar tiles, fitilu, fenti, kayan lantarki da tufafi duk kusan shagunan su ne. Akwai layi Kacokam sunan sa Igbo Road wanda saboda yawansu a wajen sunan ya koma haka.

Idan ka dawo harkar magani suna nan sun yi kaka-gida sune uwa da makarbiya a wannan fanni. Mafi muni ma shine mahaukatan kudaden da suke samu a cuwa-cuwar jabun magunguna.

Ba ruwansu da hakan zai taba lafiyar mu su dai kawai su hada jabun magani a samu kudi.

Idan ka dawo batun Matsuguni unguwa guda aka sake ware musu bayan Sabon Gari a Jaba ta su ce Inyamurai zalla. Sai tafka manyan gidajen alfarma suke yi.

Amma duk wannan bai ishe su ba sai an hada da sace mana yara kanana, a yi Garkuwa da su a sauya musu suna da addini Sannan a sayar da su a rika yi musu fyade?

Ina hukumomin kare hakkin bil Adama? Ina kungiyoyin kare hakkin mata da kananan yara? Me aka yi ya yaran a matsayin diyyar keta musu hakkokin ‘yancin walwala? Wacce diyyar aka Ba su da zata maye gurbin mutuncin ya mace karama da aka yi wa fyade ba adadi?

Daga Maje El-Hajeej Hotoro

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan