Sakamakon wani binciken masana da su ka gudanar ya nuna cewa ma’aikatan kafafen yaɗa labarai su ne su ka fi ragwanci a tsakankanin rukunin manoma da lauyoyi da kuma magina da aka yi binciken akan su.
Sakamakon binciken ya ƙara da cewa mafi yawa daga cikin ma’aikatan kafafen yaɗa labaran sau daya tal su ke iya saduwa da mace a cikin wata ɗaya.
Tun da farko wata ƙwararriyar Likita ce mai suna Kate Moyle da ta kware wajen nazarin harkar jima’i kuma mazauniyar ƙasar Amurka ce ta bayyana sakamakon binciken da aka yi game da ƙwazon mazaje a wajen saduwa da mata.
Sakamakon binciken ya kuma nuna cewa akalla kashi 67 bisa 100 na manoma su kan sadu da mace akalla sau daya a rana. Kashi 21 ma magina kuma kan sadu da mace akalla sau biyu ne a mako.
A ƙarshe sakamakon binciken ya nuna cewa lauyoyi sun fi kowa ƙaryar suna jin daɗi a lokacin saduwa da mace.