Bayan yara tara da rundunar ƴan sandan jihar Kano ta buɓutar daga jihar Anambara yayin da aka siyar da su aka sauya musu addini har ma da bautar da su, rundunar ƴan sandan jihar Anambara ta tabbatar da kuɓutar da wasu yara biyu da aka cefanar.
Jami’in hulɗa da Jama’a na rumdunar ƴan samdan jihar Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan ya ce an ceto yaran ne a Akwa babban birnin Jihar ta Anambara
Sai dai har yanzu ba’a tabbatar da ainihin yaran da aka sato ko daga Kano aka sace su ba.
Kwamishinan ƴan sandan jihar Kano ya shawarci iyayen da ƴaƴansu suka ɓata da su kai bayanai cikin gaggawa don ɗaukar mataki.
Rahoton Mujallar Matashiya
Turawa Abokai