Abdallah Yace Wannan ce Damar Enyimba Ta Karshe Ta Lashe Continental

141

Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Enyimba International dake garin Aba wato Usman Abdallah ya bayyana cewar wannan ce Damar Enyimba ta karshe ta lashe gasar cin kofin kwararru na nahiyar Afrika.

Abdallah ya bayyana hakanne bayan da aka raba yadda kowacce kungiyar kwallon kafa zata hadu da takwararta a gasar.

Saidai Enyimba anbasu kungiyar kwallon kafa ta TS Galaxy ta Afrika ta Kudu wadda take buga gasa mai daraja ta 2 a Afrika ta Kudun.

Abdallah ya kara da cewa dole sai Enyimba sun shiga taitayinsu wajen nuna babu sani babu sabo akan kungiyar domin kada ‘yan wasan na Enyimba suga karamar kungiyace su rainasu.

Haka zalika Abdallah yakara da cewar matukar kungiyar kwallon kafa ta Enyimba nason lashe wannan gasa tofa sai sun doke manyan kungiyoyin kwallon kafa.

Enyimba dai sun sami koma baya ne ta dawowa wannan gasa bayan sunyi rashin nasara agasar zakarun nahiyar Afrika inda Al Hilal ta kasar Sudan ta fitar da Enyimba.

Enyimba dai zata karbi bakuncin kungiyar kwallon kafan ta TS Galaxy a gobe Lahadi inda za a take wasan da misalin karfe 4:00 agogon Najeriya.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan