An Gano Mutumin Kano Bayan Shekara ’30’ Da Nitsewa A Kogi

66

An samo wani mutumin Kano mai suna Aminu Baita wanda da aka bayyana shi ya mutu, bayan an yi zargin ya nitse a cikin wani kogi a shekarar 1990, tuni kuma an haɗa shi da iyalinsa a ƙarshen mako.

Wata majiya daga iyalin mutumin, Yakubu Musa, ya ce Mista Baita ƙwararren jami’in kula da marasa lafiya ne, wato ‘nurse’, ya sha fama da taɓin hankali kafin ɓacewarsa daga inda aka gan shi na ƙarshe a Ɗanbatta, tafiyar kilomita 70 daga birnin Kano.

“Aminu ya “sake tashi” ‘yan makonni kaɗan. A taƙaice dai, ɗan kawuna ya dawo daga mutuwa”, in ji Mista Musa.

“Aminu haziƙin jami’in kula da marasa lafiya ne, wanda ke aiki da Ma’aikatar Lafiya ta Kano tun shekarun 1980. Bayan ya yi aure ne sai ya fara nuna wasu irin baƙin halaye.

“Ya rasa aikinsa kuma aurensa ya mutu, wannan kuma ta faru duk da ƙoƙarin sama masa magani.

“Bayan nan ne sai Aminu ya samu kansa a wani gidan kula da masu taɓin hankali a Danbatta.

“An faɗa mana cewa Aminu ya saci jiki ya fita daga gidan mahautan, ya tsunduma cikin wani kogi, daga nan ba a ƙara ganin sa ba. A matsayinmu na Musulmi, muka karɓi labarin, muka yi addu’ar Allah Ya ji ƙan sa.

“Sai kuma ga wani labari mai ban al’ajabi ya zo. Kwanan nan, wani uzuri ya sa ɗaya daga cikin yayyena, Nasidi Musa ya je karamar hukumar Toro a jihar Bauchi don ya nemi wani surukinsa da ya ɓata, wanda aka ce an yi masa ganin ƙarshe a can.

“Bai samu surukin nasa da ya ɓata ba a can. Maimakon haka, sai ya samu ɗan kawunsa wanda ya mutu, Aminu.

“Nasidi ya ba shi wannan labari mai daɗi. Maganar da na ke yanzu, Aminu yana Asibitin Kula da Masu Taɓin Hankali na Kazaure, bayan wata tawaga daga ‘yan uwa sun dawo da shi daga Toro.

“Abin sha’awa shi ne har yanzu bai manta iyayensa ba da kawunnansa, har da babana. Ya yi ta tambayar su a hanya lokacin da muke dawowa.

“Amma fa, al’ummar da Aminu ya zauna a cikin su tsawon shekaru 30 ba su ji daɗi ba da mu ka ɗauke shi daga wajensu. Daga bayanan da muka tattara, Aminu ya ji daɗi zama a iya lokacin “mutuwarsa”.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan