Ganduje Ya Ƙaddamar Da Rabon Kayan Makaranta, Litattafai Kyauta Ga Ɗaliban Kano

254

A ranar Alhamis ne gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya ƙaddamar da rabon kayan makaranta da sauran kayan koyarwa 779,522 ga ɗaliban makarantun firamare a ƙananan hukumomi 44 na jihar.

Labarai24 ta ruwaito cewa raba kayan karatun wani ɓangare ne na shirin ilimin firamare da sakandire kyauta kuma tilas na Gwamna Ganduje.

A lokacin bikin raba kayan karatun wanda aka yi a Mariri Special Primary School da ke ƙaramar hukumar Kumbotso, Gwamna Ganduje ya bayyana cewa sha’awarsa na ganin kowane yaro a jihar Kano ya samu ilimin firamare da na sakandire kyauta ita ta sa ya ɓullo da shirin.

A ta bakinsa, a ƙaramar hukumar Kumbotso kaɗai, an raba sabbin kayan makaranta 29,480 ga ɗaliban ‘yan aji ɗaya a makarantun firamare 78 da ke ƙaramar hukumar.

Ya ƙara da cewa an raba Work Books 500, litattafan Hausa 500 da katunan flashcard a yayin bikin.

Gwamnan ya ce kamar yadda sabuwar dokar ilimin firamare ta tanada, tuni gwamnatin jihar ta fara tura kuɗaɗe kai tsaye ga makarantun firamare da sakandire 1180 da ke da yawan ɗalibai 834,366, inda take tura musu Naira Miliyan N200 duk wata, Naira Biliyan N2.4 duk shekara.

Haka kuma, Gwamna Ganduje ya ƙara da cewa gwamnati ta samar da kayan makaranta ga sabbin ɗalibai 779,522 a kan kuɗi Naira Miliyan N381.

“A ƙoƙarin rage naƙasun koyarwa a ɓangaren ilimi, gwamnati ta ɗauki malamai ‘yan sa-kai 3000 don koyarwa a makarantun gwamnati da na Ƙur’ani a dukkan faɗin jihar.

“Haka kuma, gwamnatin jiha ta ɗauki malamai na musamman guda 650 don koyar da Turanci da Lissafi a makarantun Ƙurani a dukkan faɗin jihar”, Gwamna Ganduje ya bayyana haka.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan