Manoma Sun Roƙi Buhari Ya Hana Shigo Da Tumatur

180

Manoman kayan lambu a garin Gashuwa da ke jihar Yobe sun roƙi Shugaba Muhammadu Buhari da da ya hana shigo da tumatur zuwa ƙasar nan don kare manoman gida.

Manoman sun yi wannan kiran ne ranar Juma’a a wata ganawa daban-daban da Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN.

Su ka ce yawaitar shigo tumaturin gwangwani na waje zuwa kasuwannin Najeriya ba ya taimaka wa manoma da kuma sabbin kamfanonin sarrafa tumatur a ƙasar nan.

Malam Musa Maitumatur, wani manomin tumatur, ya ce shigo da tumatur ƙasar nan ya nakasa noman tumatur na gida.

“Matsalar noman kayan lambu tana farawa ne da yadda za a kula da su, da kuma ajiye amfanin, kuma ba wanda ya ke ƙoƙarin bunƙasa tumatur na gida saboda shigo da tumatur ɗin”, in ji shi.

Ali Katuzu, wani manomi, ya ce sun yi asarar fiye da kaso 50 cikin ɗari na abinda su ka noma saboda rashin kyakkyawar ajiya, yana mai ƙarawa da cewa hakan ya kan tilasta musu su yanke tumatur ɗin, su kuma shanya shi saboda rashin kayan ajiya.

Mista Katuzu ya roƙi gwamnati da ta shigo da Ƙawancen Gwamnati da na Masu Zaman Kansu, PPP, wanda zai bada damar kafa kamfanonin tumatur don haɓaka arziƙin neman tumatur a jihar.

A gudunmawarsa, Habu Sani, shi ma wani manomi, ya ce su kan girbe kayan lambun nasu ne ta hanyar noman rani a kan busasshiyar ƙasa, ya ce za su iya biyan buƙatar tumatur ta Arewa Maso Gabas gaba ɗaya idan ba don matsalar yadda za a kula da shi ba, sufuri da sarrafawa.

“Idan ana so tumatur ɗan gida ya bunƙasa, dole gwamnati ta hana shigo da tumatur na waje, kamar yadda ta yi a shinkafa.

“Tumatur ɗan gida ba zai iya yin gasa da na waje ba, dole a hana shigo da na wajen don ma’aikatun gida su bunƙasa”, in ji shi.

A ɓangarensa, Karimu Hassan, ya ce kayan lambu da ake nomawa a Gashuwa, Nguru, Dagona da Geidam za su iya ciyar da Arewa Maso Gabas gaba ɗaya, yayinda wani manomi, Manu Ibrahim ya ce ya daina noman kayan lambu saboda ba shi da riba.

“Asara muke yi saboda babu kayan ajiya da za a zuba amfanin, to a ɗan ƙanƙanin lokaci sai su ruɓe.

“Ko dai ka siyar a farashin da ba ka so ba, ko kuma ka busar da su, wanda ba ya kawo riba mai yawa.

“Dole gwamnati ta hana shigo da tumatur ɗan waje don bunƙasa noman na gida”, in ji shi.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan