Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ƙauyuka 40 A Adamawa

156

A ƙalla ƙauyuka 40 ne ambaliyar ruwa ta tafi da su a Adamawa, Dakta Muhammad Sulaiman, Babban Sakataren Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Jihar Adamawa, ADSEMA, ya tabbatar da haka ranar Asabar a Yola.

Mista Sulaiman ya ce ambaliyar ruwan ta biyo bayan samun ruwan sama kamar da bakin ƙwarya a wasu sassan jihar a kwana uku da su ka gabata.

Ya ce mafiya yawan ƙauyukan da ambaliyar ruwan ta shafa suna kan gaɓar Kogin Benue ne, inda ambaliyar ruwan ta tafi gonaki da gidaje da dama.

“A watan Agusta na bana, mun rasa mutane 15, ɗaruruwa sun rasa muhallinsu, kuma an rasa dubban gonaki da dabbobi sakamakon ambaliyar ruwan.

“A yanzu, a kwanaki uku da su ka wuce, ambaliyar ruwan ta tafi da fiye da ƙauyuka 40 ne a ƙananan hukumomi biyar na Adamawa biyo bayan ruwan sama mai ƙarfin gaske.

“Ƙananan hukumomin da ambaliyar ruwan ta shafa su ne: Fufore, Yola ta Kudu, Demsa, Numan da Girei,” in ji Shugaban na ADSEMA.

Ya roƙi hukumomin Gwamnatin Tarayya da Hukumomin Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda su ka yi alƙawarin taimakon waɗanda ambaliyar ruwan watan Agusta ta shafa da su cika alƙawuransu.

Mista Sulaiman ya ce a halin yanzu ruwan da yake a Kogin Benue ya yi yawa sosai, kuma ya raba ƙauyuka da dama daga sauran sassan jihar.

Ya ce akwai yiwuwar samun ƙarin ambaliyar ruwa, yana mai ƙarawa da cewa tuni an tura jami’an hukumar zuwa wasu yankuna da abin ya shafa don duba irin ɓannar da ambaliyar ruwan ta yi.

Game da jita-jitar da ake yaɗawa cewa ambaliyar ruwan tana da dangantaka da sakin ruwa daga Madatsar Ruwa ta Lagdo a Kamaru, Shugaban na ADSEMA ya ce ba shi da masaniya.

“Ba wani bayani a hukumance tsakanin Gwamnatin Najeriya da ta Kamaru cewa za a saki ruwa daga Madatsar Ruwa ta Lagdo.

“Amma, yawan ruwan da yake a Kogin Benue a kwanan nan ba a saba ganin Irin sa ba”, in ji Mista Sulaiman.

Haley Gajere, wani manomi daga ƙauyen Bilachi a ƙaramar hukumar Demsa ya ce gaba ɗaya ƙauyen ambaliyar ruwa ta tafi da shi.

Mista Gajere ya ce mazauna ƙauyen suna neman mafaka a maƙotan ƙauyuka, yana mai ƙarawa da cewa ruwa ya tafi da gonakinsu na shinkafa da na masara.

“A ranar Juma’a, mun girbe ɗaya daga cikin gonakinmu na shinkafa mai tsawon hekta uku da take kan gaɓar Kogin Benue, mun yi niyyar kawo shinkafar gida ranar Asabar.

“Amma, maganar da nake yi da kai yanzu, gidajenmu sun nitse, ba ma za mu iya gano inda gonakin su ke ba, saboda ko’ina an yi ambaliya”, in ji Mista Gajere.

Ƙauyukan da ambaliyar ruwan ta shafa a Demsa sun haɗa da Mbula Bilachi, Morro 1, Morro 2 da Mbumara.

Sauran su ne: Tika 1, Tika 2, Kunteri, Kuli, Tassala, and Kulasala da sauransu.

A Fufore, ƙauyukan da ambaliyar ruwan ta shafa sun haɗa da Riko, Faram-Faram, Gurore Ribadu, Tumbi’nde, Dulo Bate, Dulo Fulani da sauransu.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan