A ranar Asabar ne Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ƙaddamar da wata ƙaramar cibiyar tattara madara a ƙauyen Tassa da ke yankin ƙaramar hukumar Dawakin Kudu na jihar Kano.
Da yake jawabi a yayin ƙaddamar da cibiyar, Ministan Aikin Gona, Alhaji Sabo Nanono, ya ce cibiyar za ta yi maganin matsalolin masu siyar da madara ya kuma inganta kasuwancinsu.
Mista Nanono ya ce gwamnati za ta kafa ƙarin irin waɗannan cibiyoyi a sauran jihohin ƙasar nan don inganta tattalin arziƙin jama’a.
“Za a kafa ƙarin cibiyoyi a Gujungu da Ringim a Jigawa don a riƙa samun sabuwar madara kuma mai tsafta”, in ji shi.
Ya ƙara cewa Gwamnatin Tarayya za ta kafa rugagen Fulani don tsugunar da makiyaya a wuri ɗaya, a kuma yi maganin rikicin makiyaya da manoma.
Ya ce wannan mataki zai kuma inganta sana’ar siyar da madarar da kuma tattalin arzikin makiyaya a yankin.
Ministan ya yi kira ga Fulani a jihar Kano da sauran sassan ƙasar nan da su zauna lafiya da manoma da sauran jama’a a al’umomin da su ke zaune a cikin su.
“Na ziyarci jihohin Bauchi da Gombe kwanan nan game da wannan batu, kuma gwamnati da gaske take game da aikin”, in ji Mista Nanono.