Yadda Lakcara Makaho A BUK Ya Ciyo Motar Miliyan 8.8 A Gasar ‘Raffle Draw’

68

A ranar Juma’a ne Farfesa Jibrin Diso, wani Farfesa Masanin Ilimi a Jami’ar Bayero ta Kano, BUK, kuma makaho ya ciyo mota da kuɗinta ya kai Naira Miliyan N8.8 tare da wasu sauran mutane 699.

A lokacin da yake miƙa motar ga Mista Diso a Abuja, Babban Sakataren Ma’aikatar Kuɗi, Kasafin Kuɗi da Tsare-Tsaren Ƙasa, Ernest Umakhihe, ya ce nasarar da Mista Diso ya samu ikon Allah ne.

Da yake bada labarin yadda malamin jami’ar makaho ya ci motar ƙirar SUV, Mista Umakhihe ya bayyana cewa ya jagoranci mutum 700 na Hukumar Haɗin Gwiwa da Hukumar Bunƙasa Ci Gaba Ta Ƙasa don halartar wani taron tattaunawa a Asaba, Delta.

Ya ce bayan taron tattaunawa na kwana biyu, sai su ka kai ziyarar zumunta zuwa kamfanain haɗa motoci na Innoson Vehicles Motor, IVM, a Nnewi don ganin irin jajircewar kamfanin wajen ci gaban tattalin arziƙin ƙasar nan.

Ya ce a matsayin nuna jin daɗi bisa wannan ziyara, sai shugaban kamfanin ya ba tawagar kyautar mota ƙirar IVM Ikenga.

Babban Sakataren ya ce an samu rikici bisa yadda za a samu wanda zai cinye wannan mota a tsakanin masu gasar 700.

A ta bakinsa, don a tabbatar da mallakar wanannan mota da kuma adalci, sai hukumar ta yanke shawarar yin amfani da gasar ‘raffle draw’ inda Mista Diso ya yi nasara.

Ya ce kawai ikon Allah ne ya sa malamin makaho ya yi nasara a gasar da aka rubuta a’a guda ‘699’, sannan aka rubuta e ‘ɗaya’, farfesan ya yi sa’ar zaɓar ‘e’ kuma ya yi nasara.

Mista Umakhihe ya taya farfesan da ya ci motar murna, ya kuma gode wa IVM bisa gudummawarsu wajen ci gaban ƙasa.

Ya jaddada shirin gwamnati da jajircewarta wajen tallafa wa da ƙarfafa gwiwar masana’antun gida ta hanyar aiwatar da manufofin masana’antun gida don tabbatar da ana amfani da “Kayan da Aka yi a Najeriya”.

Da yake mayar da jawabi, Mista Diso ya gode wa ma’aikatar bisa wannan tallafi, ya kuma bayyana nasararsa a matsayin ikon Allah.

Ya ce ya gode wa Allah da ya ba shi ikon shiga wannan aiki na ƙasa inda ya samu damar shiga gasar ta ‘raffle draw’ kuma ya yi nasara.

“Ina kuma gode wa Allah bisa yadda ya yi ni makaho, sannan ya ba ni damar mayar da nakasata zuwa iyawa.

“Dole kuma in bayyana cewa ba abu ba ne mai sauƙi ga makaho ya zama farfesa a wannan ƙasa saboda ƙalubale da dama”, in ji shi.

Mista Diso, wanda ya zama makaho ne tun yana ɗan shekara biyu, ya shawarci mutane masu buƙata ta musamman da kada gwiwarsu ta yi sanyi wajen bada tasu gudunmawar wajen ci gaban ƙasar nan.

Farfesan na Ilimi ya yi kira ga gwamnatoci a dukkan matakai da su samar da damammaki ga mutane masu buƙatar ta musamman don bada gudummawa a gwamnati da shugabanci a ƙasar nan.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan